Addu'ar Kariya Daga Sharrin Shaiɗan

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin akwai wata addu'a dazan dunga yine wanda zai zama Allah yakareni daka sharrin Shaiɗan, dan da nakantashi cikin dare nayi sallah da addu'o'i amma wlh yanzu bana iyawa ga kuma kasala danakeji?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    Babban Abin da ya kamata kowa yadunga tunawa shi ne Allah maɗaukakin Sarki daya haliccemu yahalicci Shaiɗan yafimu Sanin irin gaba da kiyayyar da Shaiɗan yake mana dan haka yabamu labari kuma yashiryardamu da abubuwan dazamu samu garkuwa da tsira daka makircin Shaiɗan da kiyayyarsa dayake mana ya ce:

    إِنَّ الشَّيْطَانَ لَكُمْ عَدُوٌّ فَاتَّخِذُوهُ عَدُوًّا ۚ إِنَّمَا يَدْعُو حِزْبَهُ لِيَكُونُوا مِنْ أَصْحَابِ السَّعِيرِ

     Lallai Shaiɗan makiyine agareku nagasken gaske dan haka kuriƙeshi amatsayin abokin gabarku wanda yaki bazai kare tsakaninku dashi ba, domin yana kiran Mutanene dansu zama 'yan wuta

    Saboda yasan shi tsinannne danhaka yasha alwashin bazaije wuta shi kaɗai ba, sai yayi duk yanda zai iya dan halakar da ɗan adam suntafi wuta tare.

    Yayi rantsuwa da Allah cewa sai ya halakar da 'ya'yan Adam, amma Allah yatabbatar masa bai isa yahallakar da bayinsa nakwari nagari ba, Allah yacewa Shaiɗan.

    إِنَّ عِبَادِي لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَانٌ إِلَّا مَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْغَاوِينَ

    "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."

    Kayi ƙoƙari yakai ɗan'uwa kazamo cikin waɗanda Shaiɗan bashi da iko akansu, domin Allah yayi rantsuwa cewa sai ya cika wuta da aljanu da mutane amma waɗanda suka zama mabiya Shaiɗan.

    لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ

    Allah yayi rantsuwa dakansa cewa sai ya cika wutar jahannama da aljanu da mutane.

    Saboda haka kullum kadunga ji aranka cewa kanada wani makiyi dake biye da kai duk inda kake yasha alwashin sai ya halakar da kai amma bafa tilasta maka zaiba sharawace zaita baka inya kawo waccan kaƙi karɓa yakawo maka wata haka harsai yatabbatar yahalakar da kai baka da rabo aduniya, kadunga ji aranka 24 awa yakeyi baya bacci kawai danyaga yahalakar da kai kazamo cikin 'yan wuta.

    Shiyasa yana da matakai masu yawa dayakebi dan yaga ya halakar da ɗan adam, farko saɓon Allah yake fara baka shawarar aikatawa inya tabbatar bayanda za ayi ka saɓi Allah dagan-ganci sai ya fara saka maka kasala cikin duk wani aikin Alkhairi dakake aikatawa.

    Shiyasa Allah yabamu rigakafi akansa ya ce:

     وَإِمَّا يَنْزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ

    Duk lokacinda kaji Shaiɗan yana jefo maka wasu ayyuka na saɓo ko yana sanya maka kasala awasu ayyuka na alkhairi dakake kanemi tsari daka gareshi awajan Allah.

    Shiyasa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yakoyar damu wasu zikirori da addu'oi waɗanda zamukeyi safe dayamma dalokacin kwanciya bacci duk dansu zamto mana garkuwa da tsari daka Shaiɗan makiyinmu,

    Waɗanda bazasu ambatu a nan ba, babban abin da ake samun kariya dashi daka sharrin Shaiɗan shi ne ambaton Allah, mutum yalazumci zikiri karatun alƙur'ani hailala, tahmidi, da dukkan wasu zikirori da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yakoyar damu safe da yamma da dare da lokacin kwanciya bacci datashi daka bacci, da lokacinda zamu hau abun hawa ko zamuyi tafiya ko muka sauka awani gari amatsayin baki dana cire kaya dana sanya tufafi dana cin abunci da dukkan zikirori nayau da kullum, waɗannan suke zasu zamar maka garkuwa daka sharrin Shaiɗan da rundunarsa cikin mutane da aljanu.

    Wannan matsalar taka daka Ambata cikin tambayarka hakika dayace daka cikin matakan da Shaiɗan tsinanne yakebi wajan halakar da ɗan adam aƙoƙarinsa nacika alkawarin daya dauka da Allah cewa sai ya halakar damu, Allah maɗaukakin sarki yasanya katangar tsari tsakaninmu da Shaiɗan.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.