Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Jej Je

7.35 Na  Jej Je

Wannan ma wasa ne na yara maza da mata. Yana da zubi da tsari irin na wasan Lakkuma-Lakkuma Lale.Abin da ya bambanta su kawai shi ne waƙoƙin da ke cikin kowanne. Waƙar da ake rerawa yayin wannan wasa ita ce:

Na jej je – najej je,

Na jej je ni gidan gwauro,

Gwauro ya ba ni tuwon dusa,

Ban karɓa ba ina tsoro,

Tsoron me?

Tsoron wani abu jan baki,

Jan baki sari ƙoto,

Ƙoton me?

Ƙoton gidan baraje,

Barajen da wa yake?

Ɗauko hannu mu je mu,

Mu je mu wace rana?

Ranar tashin kalele,

Kalele-kalele,

Kalele barbaɗin tusa!

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments