Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Kale

7.34 Na Ƙale

Wannan ma wasa ne da ake ɗaurawa. Yara maza da mata kan gudanar da shi. Babu wani takamaiman wuri ko lokaci da aka ware domin wasan. Sannan wasan ba ya tafiya da waƙa. Akan gudanar da shi tsakanin mutane biyu ko sama da haka.

7.34.1 Yadda Ake Wasa

Yayin da yara suka ɗaura wannan wasa a tsakaninsu, za su riƙa lura da juna. Da zarar ɗaya ya hangi abokin wasansa da abinci, zai yi saurin furta cewa: “Na ƙale!”

Da zarar ya yi wannan furucin, to abincin ya zama mallakinsa. Saboda haka, dole abokin wasan ya miƙo masa abincin. Idan kuwa mai abincin ya riƙa kallon yaro, shi zai furta wannan furuci. Yayin da haka ta faru, to abincinsa ba zai fita daga mallakinsa ba. Ke nan dai, ya ƙale abinsa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments