Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunkuya Dundu

7.32. Sunkuya Dundu 

Wannan wasa ne na yara maza da mata. Babu wani takamaiman wuri ko lokaci da aka ware domin gudanar da shi. Sannan ba ya tafiya da waƙa. Baya ga haka, ba ya buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi. Yara biyu ma za su iya gudanar da wasan a tsakaninsu.

7.32.1 Yadda Ake Wasa

Kafin a yi wasan sunkuya dundu dole ne a ɗaura. Yadda ake ɗaurawa ko shi ne; masu wasa za su kawo hannayensu. Sannan su ko ya ƙanƙwasa yatsarsa kamar ƙugiya. Sai a lanƙaya yatsun a jikin na juna. Daga nan kowa ya ja. Da zarar an yi haka, to an ɗaura ke nan.

Daga lokacin da aka ɗaura sunkuya dundu, duk wanda ya sunkuya, abokin wasansa zai fake shi ya ɗima masa dundu. Saboda haka, kowane ɗan wasa zai riƙa lura da halin da yake ciki. Sannan ba zai sake ya sunkuya ba sai ya duba cewar abokin wasansa ba ya kusa.

7.32.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sai dai a wasu lokuta wanda aka dunda har kuka yake yi. Wasan kuma yana koyar da jarumta da juriya ga yara. Baya ga haka, yana koyar da nutsuwa da lura kafin aikata wani aiki.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments