Ticker

6/recent/ticker-posts

Lasko

7.31 Lasko

Wannan ma wasa ne na yara maza da mata. Ba ya tafiya da waƙa, sannan babu wani takamaiman lokaci ko wurin da aka ware na gudanar da wannan wasa. Ba a kuma buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi.

7.31.1 Yadda Ake Wasa

An fi gudanar da wasan lasko yayin da ƙawaye ko abokai suka haɗu a hanya. Ko kuma bayan an kamala wasa za a watse, ko yayin da wani ko wata ya kawo ziyara gidan aboki ko ƙawa. Yadda ake lasko kuwa shi ne; yayin da aka zo rabuwa, mai yin lasko zai ɗira wa abokin wasan dundu ko duka. Sannan zai ce:

“Lasko! Ranar aurenka ka rama.”

Idan mace ce kuwa za ta ce:

“Lasko! Ranar aurenki ki rama.”

Daga nan sai wanda ya yi lasko ya gudu. Dolen wanda aka yi wa lasko ya haƙura. Shi ma zai riƙe abin a zuciya, har sai ranar da ya faki wanda ya masa lasko, shi ma ya rama ya gudu.

7.31.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Wanda ya yi lasko da wanda aka yi wa lasko duka babu mai ɓata rai. Domin sun ɗauki wannan duka wasa. Duk da cewa, wani lokaci har akan samu wadda aka yi wa lasko ya yi ƙwalla ko ta yi ƙwalla. Sannan wasan na koya jarumta da juriya. Musamman kasancewar abin kunya ne mutum ya yi kuka ko nuna raki yayin da aka masa lasko.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments