Ticker

6/recent/ticker-posts

Dunguren Kule

7.29 Dunguren  Kule

Wannan wasa ne da yara maza da mata masu ƙarancin shekaru suke yi. Babu takamaiman wurin wasa da aka ware domin gudanar da shi. Sannan ba dole sai an samu taron yara ba kafin gudanar da wasan. Ba ya tafiya da waƙa, sannan ba ya buƙatar wani kayan aiki na musamman.

7.29.1 Yadda Ake Wasa

Mai yin dunguren kule zai tsuguna sannan ya kifa kansa a ƙasa, tare da dafa hannuwansa a gefe da gefen kan. Sai kuma ya ɗago ƙafafun nasa ya wuntsila ta gaba. Zai kasance ke nan ya juya, kwance bisa gadon bayansa. Yara masu ƙarancin shekaru na jin daɗin wannan wasa.

7.29.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Bayan haka yana cire wa yara tsoro. Domin kuwa duk yaro mai tsoro ba zai iya dunguren kule ba.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments