Ticker

6/recent/ticker-posts

Hajijiya

7.27 Hajijiya 

Wannan ma wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanarwa. Mutum guda ma yakan iya wannan wasa shi kaɗai. Amma akan samu yara sun taru wuri guda domin gudanar da shi. Akan gauraya wasan da waƙa a wasu lokuta. Sannan yana cikin rukunin wasannin tsaye waɗanda ba su buƙatar kayan aiki. Akan gudanar da wannan wasa a cikin gida ko dandali. Zai iya kasancewa da hantsi ko da yamma ko ma da dare, musamman lokacin farin wata.

7.27.1 Yadda Ake Wasa

Masu hajijiya za su ware hannayensu yayin da suke tsaye. Za kuma su ba da tazara a tsakanin juna gudun kada wani ya buge abokin wasansa, ko kuma ya faɗa kansa. Daga nan za su riƙa juyawa da ƙarfi tamkar fanka. A wasu lokuta sukan haɗa da waƙa kamar haka:

Hajijiya-hajijiya kama ni,

Hajijiya-hajijiya kama ni.

Haka za su ci gaba da yi har lokacin da ƙarfinsu ya ƙare ko kuma jiri ya ɗebe su. Wasu sukan faɗi. Wasu kuwa sukan kama tangaɗi cikin jiri tamkar masu maye. Jarumi a wannan wasa shi ne wanda kowa ya faɗi ya bar shi nan tsaye yana ci gaba da hajijiya.

7.27.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi a tsakanin yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Sukan kuma gwada jarumta da juriya yayin gudanar da wasan.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments