Ticker

6/recent/ticker-posts

Kumbukululu

7.21 Kumbukululu

Wannan wasa ne da yara maza da mata duka sukan gudanar da shi. Adadin yaran da ke gudanar da shi na kaiwa biyar zuwa sama da haka. A yayin gudanar da wasan, akan samu guda a matsayin kumbukululu da kuma sauran ‘yan wasa. Wannan wasan dandali ne, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, lokacin farin wata. Wasan yana tafiya da waƙa, sannan yana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Kayan aikin kuwa shi ne kallabi ko wani tsumma da za a yi amfani da shi wurin yin kumbu kululu.

7.21.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan nemi ɗankwali ko wani tsumma su rufe wa ɗaya daga cikinsu ido. Wannan rufe ido akan kira shi kumbukululu, haka ma yaro ko yarinyar da aka rufe wa idanun. Daga nan yara za su watse. Kumbu kululu kuwa za ta riƙa bi tana laluɓe da niyyar ta kama kuma ta yanka. Duk wanda kumbu kululu ta yanka, to shi/ita ce za ta zama kumbu kululu. Yara za su riƙa waƙa kamar haka:

Kumbu kululu kumbu kululu,

In kin ji hayaniya ana da yawa,

In kin ji hayaniya akwai nama.

Da zarar ta kai sura, duk yara sai su watse. Haka za ta yi ta fama har Allah Ya ba ta damar kama ɗaya daga ciki.

7.21.2 Tsokaci

Wannan wasa ne na nishaɗi wanda kuma hanya ce ta motsa jiki ga yara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments