Ticker

6/recent/ticker-posts

O Maciji

7.15 O Maciji 

Wannan wasa ne na tarayya tsakanin maza da mata. Wato maza da mata duk na gudanar da wannan wasa. Kimanin mutane goma zuwa sama ne suke gudanar da shi. Wannan wasa ne na dandali, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Wasan na tafiya da waƙa, amma ba ya buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi.

7.15.1 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su kasu kaso gida biyu, su riƙa fuskantar juna. Sannan za su riƙe hannunwan juna daga ɓangarorin guda biyu. Daga nan kuma ɗaya zai hau bisa hannuwan a kwance. Yaran za su riƙa rausaya wanda ke saman hannuwan nasu tare da yin waƙa kamar haka:

O maciji,

Zalala maciji,

Ga maciji a bakin kogi zalam.

Haka za su yi ta yi sai adadin da aka ɗiba ya ƙare. A nan wanda ke saman zai sauka/za ta sauka, wani/wata kuma ta/ya hau. Wannan wasa ne na nishaɗi da kuma motsa jiki.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments