Ticker

6/recent/ticker-posts

Boyel

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

7.14 Ɓoyel 

Wannan ma wasa ne na yara maza da mata.  Kimanin yara biyu ne ko sama da haka suke gudanar da wasan a tsakaninsu. Wasan ba ya tafiya da waƙa. Sannan akan yi amfani da wasu kayan aiki domin gudanar da shi.

7.14.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a gida ko wurin sauran yara ko dai wani wuri da yara suke taruwa.

ii. Akan gudanar da wasan  da hantsi ko da yamma. Wasu lokuta akan yi da dare amma idan akwai farin wata mai haske sosai.

7.14.2 KayanAiki

i. Ƙasa

ii. Ƙaramin dutse (tsakuwa) a matsayin ‘ya

7.14.3 Yadda Ake Wasa

Yara za su yi tsubi-tsubin ƙasa kimanin uku ko huɗu ko sama da haka. Daga nan mai tafiya zai riƙe ‘yarsa da yatsu. Zai riƙa sanya hannun da gaggawa cikin wannan tsubi-tsubin ƙasa. Zai riƙa yi cikin gaggawa yadda ba za a riƙa ganin lokacin da zai bar ‘yar a ɗaya daga cikin tsubi-tsubin ƙasar ba.

A yayin da mai tafiya ke canza ‘yar daga tsubin ƙasa zuwa wani tsubin, zai faki idon abokan wasansa ya aje ‘yar a ɗaya daga cikin tsubin ƙasar. Sai kuma a ci gaba da tamkar bai ajiye ‘yar tasa ba. Bayan ya kamala sai ya ba wa dama a bokin wasa da ya nemo tsubin da ya bar ‘yarsa. Idan ya nuna daidai, to ya ƙwace saboda haka shi zai ci gaba da tafiya. Idan kuwa bai nuna daidai ba, to wanda ke wasa ne zai ci gaba.

7.14.4 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana buƙatar nitsuwa tare da amfani da hankali domin gano haƙiƙanin gidan da mai tafiya ya bar ‘yarsa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Post a Comment

0 Comments