Ticker

6/recent/ticker-posts

Dan Mutumi-Mutumi

6.97 Ɗan Mutumi-Mutumi 

Wannan wasa ne na yara mata da ke cikin rukunin wasannin tashe. Wasan na tafiya da waƙa sannan yana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Kimanin yara uku zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. Sannan an fi yin sa da dare bayan an sha ruwa.

6.97.1 Kayan Aiki

i. Tabarma

ii. Igiya (zai iya kasancewa kallabi ko wani abin da za a iya ɗauri da shi)

iii. Hijabi

6.97.2 Yadda Ake Wasa

Yara za su samu tabarma, sai su naɗe ta a kan ɗaya daga cikinsu. Wato za su zagaya mata tabarmar kamar mayafi. Saman tabarmar zai wuce kan yarinyar sannan a naɗe shi tamkar toliyar bukka (ƙahon bukka). Bayan an ƙare tsaf, sai a sanya hijabi a kai. Hijabin da za a sanya zai kasance dogo wanda zai rufe tun daga kan saman tabarmar har ƙafafuwan yarinyar.

Yayin da yara suka isa wurin gabatar da tashe, za su fara rera waƙa tare da tafi. Yarinyar kuwa za ta durƙusa bisa guiwowinta, sannan ta fara rawa. Abin zai kasance tamkar dai ba mutum ba ce. Ga yadda waƙar take:

Ɗanmutumi-mutumi,

Ɗanmutumi nawa,

An ce ka iya rawa,

An ce ka iya juyi,

Jujjuya mu gani.

6.97.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara da kuma musamman masu kallonta.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments