Ticker

6/recent/ticker-posts

Ga KudinToshinki Na Bara

6.96 Ga KuɗinToshinki Na Bara 

Wannan ma wasan tashe ne na yara mata. Yana tafiya da waƙa, sannan ana buƙatar kayan aiki yayin da za a gudanar da shi. Kimanin yara biyar ne zuwa sama da haka suka fi gudanar da wannan wasa. Daga cikinsu akan samu Malama, sai kuma sauran masu wasa.


6.96.1 Kayan Aiki

i. Sallaya/darduma ko wani abin da ake shimfiɗawa domin a yi salla a kai

ii. Tabarma

iii. Kwallaye ko fanteku ko kwanuka ko ƙore

6.96.2 Yadda Ake Wasa

Yara za su tanadi kayan aikin da aka bayyana a ƙarƙashin 6.96.1. Yayin da suka shiga gida domin gabatar da wannan wasan tashe, za su shimfiɗa tabarma. Dukkanin yaran za su zauna sannan su ajiye languna ko kwanuka da suka zo da su a gabansu. Ɗaya daga cikinsu kuwa, wadda ake kira Malama, za ta wuce gaba kaɗan, sannan ta shimfiɗa sallaya ko wani abin sallar da suka zo da shi.

Bayan komai ya kammala, Malama za ta fara salla, amma tawasa. Za ta riƙa tsayuwa irin ta salla har da kama ƙirji. Sannan ta sunkuya kamar ta yi ruku’u. Ta sake ɗagowa, ta kuma duƙa kamar za ta yi sujada, amma goshinta ba zai taɓa ƙasa ba. Bayan haka, ba dole ne ta dubi gabas ba yayin wannan salla. Za ta iya duban kudu ko arewa ko yamma. Sannan za ta riƙa yin sallar ne cikin gaggawa.

Yaran da suke zaune bisa tabarma za su fara waƙa, ita kuwa Malama za ta riƙa amsawa yayin da take ta faman sallarta. Ga yadda abin yake kasancewa:

Bayarwa: Malama ga kuɗin toshinki,

Malama: Bankaɗa lefena ku zuba mini,

Ba na barin salla ta wuce ni.

 

Bayarwa: Malama me kike ta faɗi ne?

Malama: So nake na yi tarin salla,

Don bana kun ga ko ba a wuce ni.

 

Bayarwa: Malama ya batun tashen ne?

Malama: Tashen bana ya fi na bara samu,

Dole ne yanzu nai farawa.

 

Bayarwa: Malama me kike ta faɗi ne?

Malama: Ca nake ku taho mu yi taku,

Mui haka mui haka mui juyawa.

Bayarwa: Malama kin yi sallar safe?

Malama: Ban yi ba in kun yo taku,

Anjima ni zan yo tawa.

 

Bayarwa: Malama ashe halinki yana nan?

Malama: Kai ku ƙyaleni tashen za a yi,

Koko tambaya kuke so kui min?

 

Bayarwa: Malama ai dukka muna so,

Malama: To ku bari sai gari ya waye,

Tambayarku dole in amsawa …

Wasu lokuta masu tashe sukan ƙara wasu tambayoyi bayan waɗannan. Dukkuwa tambayoyin da amsoshin sukan kasance ne cikin waƙa.

6.96.3 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ƙwarai ga masu kallo. Musamman idan mutum ya ga yadda Malama take ta zalaƙi alhali salla take yi. Lallai kuwa ga aladar salla ga ta magana.Sannan yadda take ta faman duddungura sallar kansa abin dariya ne. Baya ga haka kuma, waƙar na ɗauke da saƙwanni daban-daban da suka kasance hannunka-mai-sanda ga masu sauraro. Wannan ya haɗa da kira zuwa ga ibada musamman ga watan azumi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments