Ticker

6/recent/ticker-posts

Farin Zoben Azurfa

6.78 Farin Zoben Azurfa

Wannan wasan yara mata ne na dandali. Saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Kimanin yara huɗu ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa. Ba ya buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi.

6.78.1 Yadda Ake Wasa

Wannan wasa yana da zubi da tsari irin na wasan Kwalba-Kwalba Dire.Abin da ya bambanta su kawai shi ne waƙoƙin da ake rerawa cikin wasannin. A wasan Farin Zoben Azurfa ana rera waƙar ne kamar haka:

Mai Direwa: Kai na farin zoben,

Masu Cilli: Farin zoben azurfa.

 

Mai Direwa: Ke da kika ce Halima tana buga miki,

Masu Cilli: Farin zoben azurfa.

 

Mai Direwa: Taro ɓalle ga Aminu na buga mini,

Masu Cilli: Farin zoben azurfa.

 

Mai Direwa: Sisi ya ɓalle ga Aminu na buga mini,

Masu Cilli: Farin zoben azurfa.

 

Mai Direwa: Ke da kika ce Khadija na buga mini,

Masu Cilli: Farin zoben azurfa.

 

Mai Direwa: In na shirya Zainab tana buga mini,

MasuCilli: Farin zoben azurfa.

 

Mai Direwa:  Ke da kika ce A’isha na buga miki,

Masu Cilli: Farin zoben azurfa.

 

Mai Direwa: In na shirya Ruƙayya na buga mini,

Masu Cilli: Farin zoben azurfa. 

Abin lura a nan shi ne, mai direwa za ta riƙa ambaton sunayen ƙawayenta ne da kuma saurayinta da sauran makusantanta. Yayin da ta ƙare waƙar, za ta koma cikin masu cilli. Wata yarinyar kuma daban za ta fito domin direwa.

6.78.2 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar musu nishaɗi da annashuwa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA 

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments