Ticker

6/recent/ticker-posts

Mama Ta Ki Shillona

6.77 Mama Ta Ƙi Shillona

Wannan ma wasan gaɗa ne na dandali mai buƙatar ‘yan wasa da dama. Misalin yara goma zuwa sama ne suke gudanar da shi. Wasan na gaɗa ne da ake gudanarwa a dandali. An fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Yana tafiya da waƙa tare da tafi. Amma ba a buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi.

6.77.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira. Sai kuma yarinya guda ta fito tsakiya. Za ta riƙa ba da waƙa sauran kuma suna amsawa tare da tafi da rangwaɗa. Waƙar ita ce kamar haka:

Bayarwa: Ayyaraye iye dije,

Amshi: Yaraye iye dije.

 

Bayarwa: Jajjage ruwan lemo,

Amshi: Arziki na Allah ne.

 

Bayarwa: Mama ta ƙi shillona,

Amshi: Baba ya ƙi shillona.

 

Bayarwa: Tunda kun ƙi shillona,

Amshi: Ni na tafi yawona.

 

Bayarwa: Ran bikin Halimana,

Amshi: Don Allah ki aika min.

 

Bayarwa: Ran bikin Umaimana,

Amshi: Don Allah ku aika min.

 

Bayarwa: Za mu je mu watsa kuɗi,

Amshi: Sai ya fi dubu hamsin.

 

Bayarwa: Za mu je mu taka rawa,

Amshi: Sai ta fi na‘yanbori.

A wannan gaɓa yara za su haɗe wuri ɗaya, su yi ta tiƙar rawa. Da zarar yarinya ta kammala wannan waƙa za ta koma cikin da’ira, wata daban kuma za ta fito.

6.77.2 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki da samar da nishaɗi ga yara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments