Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokos

6.76 Lokos

Wannan ma wasa ne na yara mata. Kimanin adadin yara uku zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Wannan wasan dandali ne, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Yana tafiya da waƙa, amma ba ya buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi.

6.76.1 Yadda Ake Wasa

Yara biyu sukan riƙe hannuwa. Ɗaya kuwa za ta je nesa kaɗan da su. Sai kuma ta dawo wurin da suke. Daga nan za ta ce:

“Locos.”

Yara biyu da riƙe da hannuwa kuwa za su ce:

“Kasuwar mata.”

Sai wannan yarinya ta tambaya:

“Nawa ne?”

Sai su ce:

“Ishirin da biyar.”

Sai kuma ta ce:

“Sha biyar.”

Sai su kuwa su ce:

“Ban ga dama ba.”

Daga nan yarinyar za ta juya kamar za ta tafi, sannan ta ce:

“To na tafi.”

Yaran kuwa za su ce:

“Haba bebi bebi zo ki hau.”

Da zarar sun faɗi haka, yarinyar za ta zo da gudu ta haye bisa hannuwansu. Su kuwa za su riƙa lila ta suna ƙirge:

Ɗaya,

Biyu,

Uku … 

Haka za a yi ta ƙirgawa har zuwa adadin da suka iyakance. Daga nan sai ta sauƙa wata kuma ta karɓa.

6.76.2 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar wa yara nishaɗi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments