Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yar Ato

6.55 ‘Yar Ato

Wannan wasa ne na yara mata. Yana da zubi da tsari irin na wasan Kwalba-Kwalba Dire.Waƙoƙin da ke cikin wasannin biyu ne kawai suka bambanta yadda ake yin su. Za ta iya yuwuwa an samu wannan canji ne a sakamakon bambancin wurin zama. Domin kuwa, an samo bayanin wasan ‘Yar Ato daga ƙasar Kebbi. Ga yadda waƙar wasan ke kasancewa:

‘Yar Ato- ‘yar Ato,

‘Yar Ato ɗiyar Ato,

Kama kunnen Ato,

Tafi Ato na kiranki.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments