Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Nakiye

6.54 Mai Naƙiye 

Wannan wasan mata ne na gaɗa. Sai dai ga dukkan alamu bai bazu a ƙasar Hausa sosai ba. An samo bayaninsa ne daga ƙasar Sakkwato. Wasan ba shi buƙatar wani kayan aiki domin gudanarwa. Sannan an fi yin sa a dandali, musamman da dare lokacin farin wata. Kimanin mutane shida ne zuwa sama da haka suke gudanar da shi. Yana cikin jerin wasannin da ake gudanarwa a tsaye.

6.54.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsaya a tsarin da’ira. Sai kuma guda yarinya guda ta fito tsakiya. Za ta riƙa ba da waƙa yayin da saura ke amsawa. Yayin da ta kammala waƙar, za ta koma cikin jerin sauran yara, wata daban kuma ta fito. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Mai naƙiye mai naƙiye,

Amshi: Mai naƙiye.

 

Bayarwa: Mai naƙiye ta ƙofar Marke,

Amshi: Mai naƙiye.

 

Bayarwa: Mai naƙiye shigo ɗaka ɗari,

Amshi: Mai naƙiye.

 

Bayarwa: Ban yarda ba ban yarda ba,

Amshi: Mai naƙiye.

 

Bayarwa: Ban yarda ba da bukkag gona,

Amshi: Mai naƙiye.

 

Bayarwa: Ban yarda ba a sangarta ni,

Amshi: Mai naƙiye.

 

Bayarwa: Ban yarda ba a sangarta na,

Amshi: Mai naƙiye.

 

Bayarwa: Ban yardaba a kai ni a baro,

Amshi: Mai naƙiye.

6.54.2 Tsokaci

Wannan waƙa tana samar da nishaɗi ga masu gudanarwa. Sannan hannunka-mai-sanda ce ga ‘ya’ya mata. Tana nuna musu yadda ya dace su guji yaudarar maza ɓata-gari.

WASANNI A ƘASAR HAUSA 

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments