Ticker

6/recent/ticker-posts

Amali Kande

6.52 Amali Kande 

Wannan wasan mata ne na dandali. Saboda haka ana gudanar da shi ne da dare, kamar dai sauran wasannin dandali. Ba ya buƙatar kayan aiki yayin gudanarwa. Sannan yana tafiya da waƙa. A mafi yawan lokuta yara da dama ke taruwa domin gudanar da shi. Adadinsu na iya kaiwa ashirin ko ma sama da haka.

6.52.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan taru a dandali. Sai su tsaya bisa tsarin da’ira. Daga nan yaran za su fara shigowa tsakiyar da’irar ɗaya bayan ɗaya suna rera waƙa. Sauran yara kuwa za su riƙa amsawa tare da tafi har da ɗan tsalle. Yayin da suka yi ɗan tsalle, za su yiwo gaba, sai kuma su sake komawa baya. Waƙar wannan wasa ta kasance kamar haka:

 

Bayarwa: Wayyo Inna wayyo Inna!

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Kowa ya kai ni ya kai kunama,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Kowa ya kai ni ya kai bala’i,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Kowa ya kai ni ya kai jafa’i,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: To an kai ɗan maciji gidansa,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Wayyo Inna wayyo Inna!

Amshi: Amali Kande.

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

6.52.2 Tsokaci

Haƙiƙa wannan wasa saƙo ne ga iyaye da ma sauran masu sauraro. Waƙar wasan tana jan hankali game da auren dole, da kuma auren wuri. Tana nuna ƙudirin mata na ta da zaune tsaye da hana ruwa gudu duk lokacin da aka musu auren dole. Wato ko dai aka aurar da su ba tare da lokacinsu ya yi ba, ko kuma aka haɗa su da mijin da ba sa so. To ke Amali Kande ba ki  yin haƙuri a sasanta?

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments