Ticker

6/recent/ticker-posts

Ni Mota Nake So

6.51 Ni Mota Nake So

Wannan ma wasan gaɗa ne da ke da buƙatar yara da yawa domin gudanarwa. Adadin masu gudanarwar na iya kaiwa ishirin ko sama da haka. Ba a buƙatar wani kayan aiki domin gudanar da shi. Sannan yana cikin rukunnen wasannin gaɗa masu tafiya da waƙa.

6.51.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Kasancewar wasan na gaɗa, an fi gudanar da shi a dandali da dare, musamman lokacin farin wata.

6.51.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira mai ɗan faɗi. Wato za su riƙa ba da ‘yar tazara tsakanin juna. Daga nan sai guda ɗaya ta fito tsakiya. Za ta riƙa ba da waƙa sauran kuma na amsawa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Ni mota nake so,

Amshi: Yayin mota ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni mashin nake so,

Amshi: Yayin mashin ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni keke nake so,

Amshi: Yayin keke ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni jirgi nake so,

Amshi: Yayin jirgi ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni allura nake so,

Amshi: Je ki gidan Malam Nagajere,

Ya iya allura talatin,

Wanda Bature bai iya ba,

Jish kankana jish kankana.

Jish kankana jish kankana.

Daga nan dukkanin masu wasa za su ɗan taka rawa. Da zarar sun ƙare, to wannan za ta koma cikin da’ira. Wata daban kuma za ta fito domin ci gaba da wasa.

6.51.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta samar da nishaɗi da kuma motsa jiki ga yara. Waƙar wasan na ɗauke da wani saƙo da ya shafi burin ‘ya’ya mata yayin aure.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments