Ticker

6/recent/ticker-posts

6.5 Muhammadu - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 138)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

6.5 Muhammadu

Wannan ma waƙa ce da ake yi a matsayin roƙon ruwa. An samu wannan waƙa daga garin Malumfashi da ke jahar Katsina. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Allah ba mu ruwa,

Amshi: Muhammad.

 

Bayarwa: ko yau ko gobe,

Amshi: Muhammad.

 

Ko tashin asuba,

Amshi: Muhammad.

 

Ko yanzu ya zubo.

Amshi: Muhammad.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments