Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
6.4 Halilu
Wannan na ɗaya daga cikin waƙoƙin roƙon ruwa da suka sanu sosai a ƙasar Hausa. Sai dai akan samu bambance-bambancen dangane da yadda ake rera waƙoƙin daga wuri zuwa wuri. Ga bisa dukkan alamu, wannan ne ya sa Ibrahim (Mrs) (2002: 106) ta yi amfani da Haliru a maimakon Halilu. Wannan na nuna, haka aka rera mata waƙar yayin da take gudanar da nata bincike. Ga yadda wannan bincike ya samo waƙar:
Bayarwa: Ruwa-ruwa-ruwa Halilu,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Ɗan sarkin ruwa,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Limamin ruwa,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Mai wandon ruwa,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Mai rigar ruwa,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Mai hular ruwa,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Takalmin ruwa,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Ka ba mu ruwa mu sha,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Gero ya bushe,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Ka ba mu ruwa mu sha,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Dawa ta bushe,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Ka ba mu ruwa mu sha,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Tsuntsu na kuka,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Ka ba mu ruwa mu sha,
Amshi: Halilu.
Bayarwa: Ruwa-ruwa-ruwa,
Amshi: Halilu.
Haka dai wannan waƙa ke ci gaba, ta hanyar lissafo abubuwan da ke buƙatar ruwa dangin shuke-shuke da kuma dabbobi. Za a lura da cewa, a cikin wannan waƙa ana roƙon wani ne mai suna Halilu a maimakon Ubangiji. Sannan ana nuna cewa shi ɗan sarkin ruwa ne, wanda suturarsa ma duka ta ruwa ce, kuma shi ke da ikon ba da ruwa. Lura da wannan, za a iya hasashen cewa, Bahaushe ya fara rera wannan waƙa tun kafin zuwan Musulunci. Babban dalili kuwa shi ne, tunanin da aka ƙulla zaren waƙar da shi, ba irin na addinin Bahaushe ba ne na Musulunci.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.