Ticker

6/recent/ticker-posts

6.6 Kammalawa - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 138)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

6.6 Kammalawa

Bahaushe bai ɗauki waƙa a matsayin hanyar samar da nishaɗi ba kawai, har ma ya sanya ta a cikin addini. Hujjar wannan batu kuwa na cikin misalan da aka kawo na waƙoƙin roƙon ruwa da ke sama, wato inda Bahaushe ke amfani da waƙoƙi domin kai kukansa zuwa ga Ubangiji game da ruwan sama. Lura da wannan, da ma wasu dalilai, lallai waƙa ta kasance wata aba mai babban matsayi ko gurbi ga rayuwar Bahaushe ta gaba ɗaya.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments