6.37 Daƙu Fara
Wannan ma wasan yara mata ne da suke gudanarwa a zaune. Yana cikin rukunnin wasannin da ba sa tafiya da waƙa. Kimanin yara shida zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.
6.37.1 Wuri Da Lokacin Wasa
i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a cikin gida.
ii. An fi gudanar da wasan da dare.
6.37.2 Yadda Ake Wasa
Yara za su zauna a jere, sannan su miƙe ƙafafunsu gaba. Ɗaya daga cikinsu kuma za ta kasance a gaba. Za ta tsuguna a gabansu tana fuskantarsu. Sai kuma ta fara taɓa yatsun ƙafafunsu kamar yadda suke jere a layi. Wato idan ta taɓa yatsun ƙafar yarinyar farko, sai kuma ta koma ta gefe da ita. Za ta riƙa yi tana cewa:
“Daƙu”
Yaran kuwa za su riƙa cewa:
“Fara”
Haka za ta yi sai ta kai ƙarshe. Daga nan kuma za ta riƙa bin su ɗaya bayan ɗaya tana musu tambayoyi. Duk wadda ta tambaya za ta ba ta amsa. Ga yadda abin yake:
Tambaya: Mene ne sunan mijinki na fari?
Amsa: Mamman
Sai mai tambayar ta ɗauki ƙasa kaɗan a hannunta ta bai wa yarinyar, sannan ta ce: “Karɓi kar Mamman ya mamme mana gari. Da ma garin ga shi da Mammaye.” Sai kuma ta ci gaba da tambaya:
Tambaya: Wace ce ƙawarki ta fari?
Amsa: Amina
A nan ma za ta sake ɗiban ƙasa kaɗan ta ba ta. Sannan ta ce: “Karɓi kar Amina ta Amino mana gari. Da ma ga shi garin da Aminuwaye.”
Tambaya: Wace ce yayarki ta fari?
Amsa: Talatu
Za ta sake ba ta ƙasa, sannan ta ce: “Karɓi kar Talatu ta Talato mana gari. Da ma ga shi garin da Talatoci.”
Tambaya: Wace ce ƙanuwarki ta fari?
Amsa: Maimuna
Za ta sake ba ta ƙasa sannan ta ce: “Karɓi kada Maimuna ta Maimuno mana gari. Da ma ga shi garin da Maimunoni.”
Da zarar an kawo wannan gaɓa, mai tambaya za ta wuce zuwa ga yarinya ta gaba. Haka za a ci gaba da yi, har sai an yi wa kowa.
6.37.3 Tsokaci
Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan saƙo ne ga iyayen yara musamman ta fuskar bayyana musu samarin da ‘ya’yansu (mata) ke soyayya da su.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.