Ticker

6/recent/ticker-posts

Ruwan Kauye

6.36 Ruwan Ƙauye

Wannan wasan gaɗa ne da ke kama da kwalba-kwalba dire. Yawanci masu wasa biyar ne ke gudanar da shi.

6.36.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Wannan wasan dandali ne. Don haka an fi gudanar da shi da dare, lokacin farin wata.

6.36.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su jeru a layi ɗaya. Ɗaya daga ciki za ta kasance a gaban layi. Wadda take gaban layin za ta riƙa faɗawa jikin waɗanda suke jere. Su kuwa za su riƙa café ta kafin ta je ƙasa, sannan su turo ta gaba. Haka za su ci gaba da yi tare da tafi da kuma waƙa. Babu wani suna takamaimai da aka ba wa wadda take tsayuwa a gaba, haka ma waɗanda ke cikin layi. Amma a nan, za a ba su suna saboda da a ji daɗin tantancewa. Saboda haka, an kira mai tsayuwa gaba da suna mai direwa, waɗanda ke tsaye layi kuma masu cafewa. Ga waƙar kamar haka:

Masu Cafewa: Ruwan ƙauye,

Ruwan ƙauye.

Mai Direwa: Jagwalgwale ne.

 

Masu Cafewa: A wanki kare a wanki doki,

Mai Direwa: A ɗauko ɗan mutum a jefa.

 

Masu Cafewa: Yarinya bakki da yayu ne?

Mai Direwa: Yayuna sun fi ɗari goma.

 

Masu Cafewa: Iya lissafa mu ji labari,

 

A wannan gaɓa, mai direwa za ta fara lissafo sunayen yayunta ɗaya bayan ɗaya a sigar muryar waƙe. Saura kuwa za su ci gaba da amsawa. Misali:

Mai Direwa: Ramlatu,

Masu Cafewa: Ta iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Khalid,

Masu Cafewa: Ya iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Halima,

Masu Cafewa: Ta iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Abdul,

MasuCafewa: Ya iya aikin Jos.

 

Mai Direwa: Ni ma na iya aikin bariki, bariki balle aikin Jos.

Da zarar an kawo wannan gaɓa to mai direwa ta kammala yin ta. Daga nan za ta koma cikin masu cafewa, wata daban kuma ta fito.

6.36.3 Tsokaci

Wannan wasa na taimakon yara wurin motsa jiki. Sannan wasan na nuna matsayin ‘yanuwantaka da kimarsa da kasancewarsa abin alfahari.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments