Ticker

6/recent/ticker-posts

Rurujina

6.35 Rurujina 

Wannan wasa ne da yara mata ke gudanarwa. Yana ɗaya daga cikin wasannin zaune. Kimanin yara biyu zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yawansu na iya kaiwa goma ko ma sama da haka. Sannan yana tafiya da waƙa.

6.35.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a wurin jaura, ko makarantun boko (lokacin shan iska)

ii. Wannan wasa ana yin sa da dare ko da hantsi ko da yamma duka.

6.35.2 Yadda Ake Wasa

Yara za su zauna a tsarin da’ira, sannan kusa da juna. Daga nan kowace za ta kifa hannuwanta a ƙasa. Wato tafin hannuwanta su kasance a ƙasa. Sai kuma a fara waƙa a tare. Yayin da ake waƙar, masu wasa za su riƙa buɗe tafukan hannayen nasu (wato bayan hannuwansu su kasance a ƙasa) sannan suna rufewa, a tare. Duk wadda ta ɓata, to za ta koma gefe. Haka za a yi ta yi har sai ya rage saura mutane biyu. Yayin da ɗayarsu ta ɓata, nan ne wasa ta je ƙarshe. Sai kuma a sake daga fari ko a canza wani wasan. Waƙar wannan wasa ita ce:

Rurujina,

Rujina-rujina,

Rujina rub!

Wawagina,

Wagina-wagina,

Wawwaginawa.

6.35.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana ɗaya daga cikin wasannin da ke samar da nutsuwa. Domin dole ne mai wasa ta nutsu don kada ta kuskure wa lokacin buɗe hannu ko rufewa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments