Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwalba-Kwalba Dire

6.34 Kwalba-Kwalba Dire

Wannan ma wasan gaɗa ne na dandali. Mutane biyar ne suka fi gudanar da shi. Amma wani lokaci yawan masu wasan na wuce haka.

6.34.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Kasancewar wasan na dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

6.34.2 Yadda Ake Wasa

Yayin da ake wannan wasa tsakanin yara biyar, guda huɗu za su tsaya su mannu da juna. Wadda za ta dire kuwa, za ta kasance a gabansu, ta juya musu baya. Daga nan za su fara waƙa da tafi. Mai direwa za ta riƙa faɗuwa jikin masu cilli, su kuwa za su riƙa riƙe ta ba tare da ta kai ga faɗuwa ƙasa ba. Sai kuma su ɗago tasu cilla ta gaba. Da zarar ta dire kuma za ta sake dawowa ta faɗo jikinsu. Ga nan yadda waƙar take:

Masu Cilli: Kwalba-kwalba dire,

Mai Direwa: Ni ba zan dire ba,

Sai na ga Magaji,

Magajin Magajiya,

Mai hawa kujera,

Ya raɓarɓashi kaji,

Hanji na iyaye,

Hanta ta maƙwabta,

Sauran kuma nawa.

A wannan gaɓa masu cilli za su riƙa ambaton rukunin jama’a daban-daban, mai direwa kuwa za ta kokkoyi salon tafiyar wadda aka ambata. Ga yadda abin yake:

Masu Cilli: Tafiyar sojoji,

Mai Direwa: Ci naga-naga naga-naga Dadan Hasiya.

MasuCilli: Tafiyar Yansanda,

Mai Direwa: Ci naga-naga naga-naga Dadan Hasiya.

MasuCilli: Tafiyar maigoyo,

Mai Direwa: Ci naga-naga naga-naga Dadan Hasiya.

MasuCilli: Tafiyar mai mashin,

Mai Direwa: Ci naga-naga naga-naga Dadan Hasiya.

MasuCilli: Tafiyar babanki,

Mai Direwa: Nan kuɗi, nan kuɗi nan banki,

Ya cika.

Da zarar an zo wannan gaɓa, to yin mai direwa ya ƙare. sai ta koma cikin ‘yan cilli wata kuma ta fito domin direwa.

6.34.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki tare da samar da nishaɗi da annashuwa ga yara. Sannan tana ɗauke da wani saƙo game da burin kowace ‘ya mace na samun aure a gidan wadata. Kamar yadda mai direwa ba za ta dire ba har sai ta ga Magaji … Sannan wasan na nuna Adabin ɗabi’un wasu gidaje game da haƙƙin maƙwabtaka da na iyaye.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments