Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
6.2 Ma’anar Jigo
Masana
da manazarta waƙoƙin sun bayar da ma’anoni a kan jigo gwargwadon yadda kowa
ke kallon kalmar da ƙumshiyar
ma’anarta. Na dubi waɗannan
ma’anonin domin gina tawa fahimta a kan jigo. Ga wasu daga ra’ayoyin masana:
Umar (1984) a kundinsa cewa ya yi:
“Jigo kalma ce da manazarta adabin Hausa suka yarda su riƙa amfani da ita wajan ambaton saƙon da waƙa ke ɗauke da shi”.
Bayanin wannan masani na nuna kalmar jigo a waƙa kalmar fannu ce da malamai da manazarta suka aminta su yi amfani da ita wajen bayyana saƙon waƙa. Wato ke nan saƙon da waƙa take ɗauke da shi shi ne jigo.
Wani manazarci
ya bayar da ma’anar jigo a kundinsa yana cewa:
“Duk lokacin da mawaƙi ya wallafa waƙa, akwai wani muhimmin abu da yake son ya isar ga masu sauraro, ko masu karatu wato saƙo. Wannan saƙo kuwa zai iya kasancewa darasi ko wa’azi ko dai wata magana a kan sauran al’amurran duniya, irin wannan shi ake kira jigo” Jangebe (1991).
A fahimtar wannan malami muhimmin abin da waƙa take ɗauke da shi shi wato muhimmin saƙo shi ne jigo. Malamin bai yi la’akari da ƙananan saƙonni ba waɗanda su ma jigogi ne sai dai ƙanana.
Sai dai Gusau cewa ya yi:
“Turke shi ne abin da waƙa take magana a kansa wanda ya ratsa tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta. Gusau (2003: 28).
Shi wannan malami ga bayar da ma’anarsa ya ambaci turke wato sunan jigo a waƙar baka a matsayin wani abin da waƙa ke zance kansa tun daga farko har zuwa ƙarshe, wato har da ƙananan batutuwa da waƙar ta ƙunsa. Ya kwatanta wanan da silalin zare na tunani, wato wanda ke tafiya ba tare da tsinkewa ba.
Yahya
ganin yake jigo shi ne:
“Jigo a fagen waƙa yana nufin saƙo ko manufa ko bayani ko ruhin da waƙa ta ƙunsa wanda kuma shi ne abin da waƙar ke son isarwa ga mai saurare ko karatu ko nazarinta” Yahya (1994:75).
Shi ma kamar sauran da suka gabata ya mabaci kalmomi masu makusanciyar ma’ana kamar saƙo da manufa da ruhi wanda ke ƙunshe cikin waƙa a matsayin jigo da sharaɗin wannan ya kasance shi ne mawaƙi ke son sadarwa ga mai saurare. Wato ke nan ko da mai saurare ya fahimci wani abu saɓanin abinda mawaƙi ke nufi, to ba zai kira wannan jigo ba domin ba shi ake son ya fahimta ba.
Ta la’akari da ma’anonin da masana
da manazarta suka ba kalmar jigo a nazarin waƙa ana iya cewa jigo shi ne ƙudurin zuciyar
mawaƙi da yake son ya bayyanar ga mai sauraro ko kuma karatu
da nufin su fahimce shi su amince da shi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.