6.25 Laula Amarya
Wannan wasa ne da yara mata ke gudanarwa a lokacin bukukuwan aure. Kimanin yara goma zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yawan nasu ya danganta da irin taron da aka yi a auren, wanda hakan na da alaƙa da yawan ƙawaye da amaryar ke da su.
6.25.1 Wuri Da LokacinWasa
i. Ana gudar da wannan wasa ne a gidajen Bukukuwan aure. Sai dai ba a wuri ɗaya ake tsayawa ba. Akan fara tun daga gidansu amarya yayin da za a kai ta ɗakinta, har zuwa gidan mijin nata.
ii. Akan gudanar da wannan wasa ne da dare ko dai duk wani lokacin da za a kai amarya ɗakinta.
6.25.2 Yadda Ake Wasa
Yara mata (waɗanda yawanci ƙawayen amarya ne) sukan taru yayin da za a raka amarya zuwa gidanta. Daga nan za su fara waƙa tare da tafi. Wata ko wasu daga cikin yaran za su riƙa ba da waƙa, saura kuwa suna amsawa tare da tafi. Waƙar da ake yi ita ce:
Bayarwa: Laula amarya,
Amshi: Laula.
Bayarwa: Bari kuka ƙanuwata,
Amshi: Laula.
Bayarwa: Bari kuka yarinya,
Amshi: Laula.
Bayarwa: Ba aure zan miki ba,
Amshi: Laula.
Bayarwa: Makaranta zan kai ki,
Amshi: Laula.
Bayarwa: Makarantar masu gari.
Amshi: Laula.
6.25.3 Tsokaci
Wannan waƙa na samar da nishaɗi da annashuwa ga yara. Bayan haka, waƙar na ɗauke da wani saƙo na faɗakarwa ga amarya, cewa aure makaranta ce. Sannan tana ba da haƙuri da kwantar wa amarya hankali.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.