Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Daura Kallabi

6.24 Na Ɗaura Kallabi

Wannan ma wasan dandali ne na mata. Wannan wasan ma na buƙatar adadin yara da yawa. Dole yawansu ya kasance daga ishirin zuwa sama.

6.24.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan gudanar da shi a makarantu ko gidajen bikin da aka samu taron yara mata.

ii. An fi gudanar da wasan da dare, ko lokutan makaranta.

6.24.2 Kayan Aiki

Kallabi/Kwali/Ɗankwali

6.24.3 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira. Daga nan biyu daga cikinsu za su shiga tsakiya. Ɗaya daga cikin waɗanda ke tsakiya za ta yi gwaggwaro ta cokara kallabinta a goshi. Daga nan wadda ta cokara kallabi za ta riƙa waƙa yayin da sauran kuma suke amsawa. Sannan waɗanda ke bisa da’irar za su riƙa zagayawa tare da tafi. Waƙar ita ce kamar haka:

Mai Waƙa: Na ɗaura kallabi,

Kallabin rashin kunya.

‘Yan Wasa: Alo.

Mai Waƙa: Sai Sa’a ta ture min.

‘Yan Wasa: Alo.

A wannan gaci, ɗayar da ke tsaye a tsakiya za ta ture kallabin da mai waƙar ta cokara kanta. Daga nan kuma za a ci gaba da waƙa:

Mai Waƙa: Ko ubanta wane ne.

‘Yan Wasa: Alo.

Mai Waƙa: Ko ubanta sarki ne.

‘Yan Wasa: Alo.

Mai Waƙa: Ba sarki ba ko Gwamna,

‘Yan Wasa: Alo.

Mai Waƙa: Ba gwamna ba ko shugan ƙasa,

‘Yan Amshi: Yaraye,

Mai Waƙa: Da wa ne nake faɗi,

‘Yan Amshi: Yaraye,

Mai Waƙa: Da Fatinake faɗi,

Sai ta zo mu ɗan girgiza kaɗan,

Girgizar da ba kunya.

‘Yan Amshi: Alo.

Daga nan za su ɗan yi rawa ita da wadda ta ambaci sunanta. Yayin da suka ƙare wannan rawa, to sai mai waƙa ta fita wata kuma ta shigo.

6.24.4 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta samar da nishaɗi da raha da kuma motsa jiki ga yara mata.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments