Ticker

6/recent/ticker-posts

Ladidin Baba

6.23 Ladidin Baba

Wannan ma wasa ne na dandali. Amma yanzu da makarantu suka yawaita, yara mata na yawan gudanar da wannan wasa a makarantu. Kimanin mutane ishirin zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yawansu na iya kaiwa talatin ko sama da haka.

6.23.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan gudanar da shi a makarantu ko gidajen biki da aka samu taron yara mata.

ii. An fi gudanar da wasan da dare, ko lokutan makaranta.

6.23.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan kasance a da’ira. Yara biyu kuma sukan kasance a tsakiya. Daga nan yaran da ke bisa da’ira za su fara tafiya suna zagaya waɗanda suke tsakiya, tare da tafi. Ɗaya daga cikin waɗanda ke tsakiya kuma za ta riƙa nuna‘yaruwarta cikin zolaya, yayin da ake waƙa, tamkar dai waƙar a kanta take magana. Yayin da aka gama waƙar, to wadda ke nuni za ta fita ta koma cikin da’ira. Wata kuma za ta dawo tsakiya, inda ɗayar za ta riƙa nuna ta yayin da ake waƙa.

6.23.3 Waƙar Wasa

Ladidin baba,

Ta ci tuwonta da manta da yajinta,

Wa zai wanke kwanon?

Wanda ya raina ubansa ɓarawo ne,

Ga abin mamaki,

‘Yar akuya da wanke-wanke,

Har da omon goma,

Had da zama a kan kujera,

Baba ka cuce ni,

Tun da ka kai ni Kwantagora,

Kwantagora gari ne,

Amma ba garin zuwa ba,

Daga mai shan taba,

Sai mai shan giya da ƙwaya,

Ƙarfi ya ƙare sai an tokara da sanda.

6.23.4 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta samar da nishaɗi da kuma motsa jiki ga yara. Sannan waƙar da ke cikin wasan na hannunka-mai-sanda zuwa ga barin wasu halaye na ƙi da suka haɗa da raina iyaye da kuma shaye-shaye irin na giya da ƙwaya.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments