Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yar Gala-Gala

6.22 ‘Yar Gala-Gala

Wannan ma wasa ne dangin bena. Sai dai zubi da tsarinsa ya bambanta da na bena. Adadin masu gudanarwa na farawa daga biyu zuwa sama da haka.

6.20.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. An fi gudanar da wannan wasa a dandali.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma, musamman da farkon damina.

6.22.2 Kayan Aiki

Ƙaramin dutse ko fashasshiyar kwalba ko makamantansu a matsayin ‘yar jifa.

6.22.3 Yadda Ake Wasa

Akan yi amfani da guntun kara ko ƙaramin itace a zana gidan dara manya a ƙasa. Gidajen akan yi su ne a jere da juna. Yawansu na iya kasancewa shida ko sama da haka. Mai tafiya za ta jefa ‘yar tafiyarta a gidan farko. Daga nan za ta fara tafiya tamkar dai yadda ake yi a bena. Da zarar an kamala gidaje gaba ɗaya, to za a yi talle. Wadda ta ci nasarar talle, to za ta sayi gida, cikin salon sayen gida a wasan bena da aka tattauna a sama.

6.22.4 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana koyar da ƙwarewar seti wajen jifa. Baya ga haka, wasan yana koyar da nutsuwa, kamar yadda rashin nutsuwa kan kai ga mai wasan ta faɗi cikin gaggawa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments