6.20 Bena
Wannan ma wasan yara mata ne na dandali. Adadin yaran da ke gudanar da shi na iya farawa daga biyu zuwa sama da haka.
6.20.1 Wuri Da Lokacin Wasa
i. An fi gudanar da wannan wasa a dandali.
ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma, musamman da farkon damina.
6.20.2 Kayan Aiki
Ƙaramin dutse ko fashasshiyar kwalba ko makamantansu a matsayin ‘yar jifa.
6.20.3 Yadda Ake Wasa
Akan yi amfani da guntun kara ko ƙaramin ita ce a zana gidan dara manya a ƙasa. Yakan kasance layuka biyu a jere. Kowane layi zai iya kasancewa uku ko huɗu ko biyar ko shida. Wato gidajen za su kasance daga shida zuwa goma sha biyu.
Kowacce daga cikin ‘yan wasa za ta ɗauko ‘yar jifa. Akan yi amfani da dutse ko fashasshiyar kwalba ko makamancinsu a matsayin ‘yar jifa. Mai tafiya za ta sanya ‘yar jifarta a gidan farko. Za ta tsalleke gidan farkon (Wanda‘yar jifarta ke ciki), yayin da ta ɗangale ƙafa ɗaya. Yayin da mai wasa ta sauƙe ƙafar da ta ɗage to ta faɗi. Wasu lokuta dokar wasa takan ba da dammar canji. Idan wasa ya kasance ‘yar canjel, to mai wasa na da damar canja ƙafar da ta ɗage yayin wasa.
Haka mai wasa za ta riƙa tsalle gida ɗaɗɗaya har sai ta je ta zagayo ƙarshen gidajen da aka zana. Yayin da ta dawo, to ta wuce gidan ɗaya. Daga nan mai wasa za ta ɗauki ‘ya ta jefa ta gidan biyu. Idan ‘yar ta shiga daidai, to za ta ci gaba da wasa, idan kuwa ta shiga wani gida, to ta faɗi. Idan kuwa layi ta hau, to sakel ke nan, saboda haka za ta sake jifa. Yayin da mai wasa ta jefa daidai, za ta ci gaba da tafiya. Duk lokacin da take tafiya, ba za ta taka gidan ‘yarta ba. Wato za ta tsallake gidan ne.
Haka mai wasa za ta ci gaba da yi, har ta je gidan ƙarshe. Yayin da ta fita a gidan ƙarshe, to za ta yi talle. Wannan ya danganta da randa nawa dokar wasa ta ƙayyade za a yi kafin talle. Mai talle za ta sanya‘yar jifarta a kan bayan hannu, sannan ta ɗangale ƙafa ɗaya ta zagayo gidajen gaba ɗaya. Za ta yi haka har sau uku. Idan‘yar jifarta ta faɗi yayin wannan zagaye to ta faɗi. Idan kuwa ta ci, to za ta sayi gida. Yayin sayen gida, mai wasa za ta juya wa gidaje baya. Daga nan za ta jefa ‘yarta baya, ba tare da ta duba ba. Duk gidan da ‘yar ta faɗa, to ta sayi wannan gida.
Yayin da mai wasa ta sayi gida, abokan wasanta ba su da daman shiga wannan gida, sai da izininta. Haka za a ci gaba da wasa tare da sayen gidaje, har a tashi a wasa.
6.20.4 Wasu Dokokin Wasa
i. Duk wadda ta taka layi ta faɗi.
ii. Duk wadda ta taka wani gida na daban da wadda ya kamata ta taka, ta faɗi.
iii. Wadda ta jefa ‘yar jifa kan layi yayin sayen gida, to za ta sake jifa.
iv. Wadda ta jefa ‘yar jifa waje yayin sayen gida, ta faɗi, kuma sai ta sake talla idan yin ta ya zagayo.
v. Masu wasa ba su da damar taka gidan da aka saya ba tare da izinin mai gidan ba.
6.20.5 Tsokaci
Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana koyar da ƙwarewar seti wajen jifa. Baya ga haka, wasan yana koyar da nutsuwa, kamar yadda rashin nutsuwa kan kai ga mai wasa ta faɗi cikin gaggawa.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.