6.19 A Fim-Fim-Fim
Wannan wasa ne da za a iya hasashen ya samu ba da jimawa ba. Wato bai samu ba sai bayan boko ya yaɗu sosai a ƙasar Hausa. Za a iya kallon hakan daga cikin irin kalaman Ingilishi da ake amfani da su yayin gudanar da wannan wasa.
6.19.1 Wuri Da Lokacin Wasa
Kasancewar wasan na zamani, an fi gudanar da shi a makarantu, musamman na sakandare da firamare. Sai dai akan gudanar da shi a dandali, musamman idan aka samu taron yaran da sun koye shi daga makaranta. Sannan akan yi wannan wasa a gidan biki.
6.19.2 Yadda Ake Wasa
Yara daga huɗu zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yawansu zai iya kasancewa har goma ko ma sama da haka. Amma mutane huɗu ne suke yi a lokaci guda. A yayin da suke yi, sauran za su tsaya su zuba musu idanu. Yayin da ɗaya ta faɗi, sai ta fita wata kuma ta maye gurbinta.
Yara huɗu za su tsaya suna fuskantar juna daga kusurwoyi huɗu. Wato biyu suna fuskantar juna, haka ma ragowar biyun. Daga nan za su fara tafi da kuma waƙa kamar haka:
Wan,
Tu,
Tiri,
Fo.
Daga nan kuma za su fara tafawa da juna cikin canza salo. Akan yi tafin ta gaba da ta gefen hagu da gefen dama. Yayin da ake wannan tafi, za a riƙa waƙa kamar haka:
Ges-ges-ges,
Tu zeiz,
Tu ze west,
Tu left an rayit,
Gib mi dokto,
Ba ni askirin ba ni firinta,
A fim-fim-fim.
Daga nan kuma za a fara lissafo abacada na Turanci har zuwa /z/. Yayin da ake yi, wadda ta faɗi za ta fita, yayin da ta gefenta za ta shigo a ci gaba.
6.19.3 Tsokaci
Wannan wasa hanya ce ta motsa jini tare da nishaɗi ga yara. Sannan wasa ne mai buƙatar nutsuwa, saboda haka, yana sanya nutsuwa ga yara.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.