6.17 Ɗan Balum-Balum
Wannan wasa ne da yara mata ke yi. ‘Yan shekarar bakwai zuwa sama ne suke wannan wasa. Akan yi wasan tsakanin yara adadin da ya fara daga biyu zuwa sama. Duk yawan yara za su iya yi.
6.17.1 Wuri Da Lokacin Wasa
i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan yi shi a wurin da aka sami taron yara. Kamar wurin niƙa ko wurin talla ko sana’a.
ii. Akan gudanar da wasan da hantsi ko da yamma ko da dare. Wasan dare an fi yin sa a dandali.
6.17.2 Yadda Ake Wasa
Fes ita ce za ta fara wasa. Masu wasa gaba ɗaya za su tsaya a layi. Fes da Sekon za su fito gaban layi, su fuskanci juna. Daga nan kowace za ta riƙe kunkumi. Daga nan fes za ta fara waƙa Sekon kuma tana amsawa.
Fes: Sima ban sisina
Sekon: Na hana!
Fes: Abin na faɗa ne?
Sekon: Dambe ne!
Fes: Har da murguɗa baki?
Sekon: Har ido!
Daga nan za su fara tafi da ‘yan tsalle-tsalle. Sannan su fara waƙa a tare tare da tafi. Ga waƙar kamar haka:
Ɗan balum-balum,
Ko kuma ɗanmu cancaɗe?
Ko kuma ɗakin Hajiya?
Ko kuma kafaɗar kare?
A yayin da suke wannan waƙa za su riƙa tafi da kuma tsalle, tare da buɗe ƙafa ko tsukewa a lokaci guda. Yayin da suka buɗe a tare sau uku, to an ƙwace wadda take yi. Haka ma idan sun tsuke a tare sau uku. Idan kuwa suka yi ta saɓanin buɗewa da tsukewa, to kuwa wadda take yi za ta ci gaba, har sai ta fita. Za ta iya kasancewa randa uku ake yi kafin a fita ko dai wani adadi da aka iyakance. Wadda ta fita za ta tsaya a gefe ta sa namujiya yayin da saura suke ci gaba da wasa.
6.17.3 Tsokaci
Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki. Waƙar farko ta cikin wasan ta fara da sigar faɗa. Amma baƙar magana da ake tsarmawa cikin sigar barkwanci na nuna wasa ne. Kamar yadda mai sekon ke cewa har ido take murguɗawa ba baki kawai ba. Ko yaya ake murguɗa ido? Sannan wannan wasa yana ƙara danƙon zumunci tsakanin yara da ‘yammata.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.