Ticker

6/recent/ticker-posts

Digi-Digi

6.16 Digi-Digi

Wannan ma wasan tsaye ne wanda yara mata misalin yara huɗu zuwa sama ke gudanarwa. Mutane da yawa za su iya gudanar da wannan wasa a lokaci guda, har misalin yara ashirin ko sama da haka.

6.16.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa da a dandali.

ii. An fi gudanar da wannan wasa da dare. Amma musamman yanzu a zamanance, akan gudanar da shi a makarantun boko.

6.16.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su tsaya a tsarin da’ira. Daga nan fes za ta fara ba da waƙa saura na amsawa. Yayin da take waƙar, za ta riƙa taɓa masu wasa ɗaya bayan ɗaya bisa tsarin layin da suke tsaye. Za ta fara taɓawar daga gefen damanta. Wadda waƙa ta tsaya a kanta, to za ta fita.

Dije: Digi-digi

Amshi: Dongi-dongi

 

Dije: Et rayit a wut,

Amshi: Go. 

Wadda ta rage ta ƙarshe ba ta fita ba, to ita ce za ta yi kamu. Mai kamu za ta ba wa waɗanda suka fita rata. Bayan sun yi ɗan nisa sai ta tambaya da cewa: “Ta zo?” Idan waɗanda suka fita sun shirya za su ce: “Eh!” Idan kuwa ba su shirya ba za su ce: “A’a!” Daga nan mai kamu za ta ce: “Ga ni nan zuwa!” Sai kuma ta bi su da gudu.

Yara za su yi ta gudu yayin da mai kamu ke bin su. Duk wadda mai kamu ta iso za ta shaye ta hanyar shafa kanta. Duk wadda mai kamu ta shafa kanta, ita ma ta koma mai kamu. A haka masu kamu za su yi ta bin saura har sai an shaye kowa daga cikinsu. Akwai iyakar fili da ake warewa wanda ba a yarda masu wasa su fita daga ciki ba. Duk wadda ta fita, to ta zama wadda aka shaye.

6.16.3 Sakamakon Wasa

Sakamakon wannan wasa shi ne kasance wa mai kamu. Wadda ta yi na ƙarshe ita ke kasancewa ‘yar kamu. Sakamakon duk wadda aka shaye ma shi ne kamu.

6.16.4 Tsokaci

Wannan wasan yana samar da nishaɗi tsakanin yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki ga yara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments