Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yar Ramel

6.14 ‘Yar Ramel 

Wannan ma wasan mata ne da suke gudanarwa a zaune. Yarinya ɗaya ma za ta iya yin wannan wasa. Sai dai an fi yi tsakanin yara biyu zuwa sama. Mata ‘yan kimanin shekaru takwas zuwa sama ne suke wasan ‘yar ramel.

6.14.1 Wuri Da LokacinWasa

i. Akan yi wasan ‘yar ramel a cikin inuwa a dandali ko a ƙofar gida ko a cikin gida. An fi gudanar da wasan a ƙarƙashin inuwar bishiya, kasancewarsa wasan zaune.

ii. Ana gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma. Ba a yin sa da dare.

6.14.2 KayanAiki

i. Duwatsu ƙanana

6.14.3 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsinto duwatsu ƙanana guda goma (10). Daga nan za su tona ɗan ƙaramin rami ko a ce gurbi, sai kuma su sanya duwatsun ciki. Kowace cikinsu za ta nemo ƙodonta, wadda da shi za ta riƙa cilli. Fes ita ce ke da hurumin sanya dokokin wasa. Dokar za ta iya kasancewa ‘yar randa ɗaya ko ‘yar randa biyu har dai zuwa ‘yar randa tara.

Bayan an kamala dukkanin tsare-tsare, sai fes ta fara. Za ta riƙa wurga ƙodago sannan ta jawo‘ya’yan da ke cikin rami da hannun da ta yi cillin cikin gaggawa, sai kuma ta cafe ƙodagon. Idan wasan ‘yar ɗaukel ce, to za ta ɗauki adadin ‘ya’ya daidai da yadda yin ta yake; wato ko dai ta ɗauki ɗa ɗaya idan tana ɗayalwa ko ta ɗauki biyu idan tana biyulwa… Sai kuma ta sake jefa ƙodo sama sannan ta ture ragowar duwatsun zuwa cikin rami. Idan kuwa dokar wasar‘yar turel ce, to za ta sake cilla ƙodonta sannan ta ture iyaka ‘ya’yan da ya da ce su koma rami, ta bar saura kuma a waje.

Yayin da mai yi ta faɗi, sai wadda take layi ta karɓa. Idan yin ta ya sake zagayowa, za ta faro daga farko idan ‘yar zubewa ce, wato ke nan waɗanda ta yi a baya sun zube. Idan kuwa ba ‘yar zubewa ba ce, to za ta ci gaba daga wurin da ta tsaya (misali ukul wan randa huɗu). Wadda take ɗayalwa, ‘ya’ya tara za ta mayar rami bayan ta jawo. Wadda take biyulwa kuwa, ‘ya’ya takwas za ta mayar, mai ukulwa ta miyar ‘ya’ya bakwai… Yayin da aka kai gomalwa kuwa, za a jawo‘ya’yan gaba ɗaya daga rami. Sai kuma a riƙa mayar da su ɗaya bayan ɗaya, har su ƙare baki ɗaya. Daga nan sai a shiga wata randa, idan randunan ba su ƙare ba.

A lokacin da ake gudanar da wasa, kowace mai wasa za ta mayar da hankali don ganin yadda bubu wan ke gudana. Idan ana ‘yar ɗauka ne, yayin da mai yi ta zo tura sauran ‘ya’ya rami bayan ta ɗauki na ɗauka, sai kuma wani ɗa ko ‘ya’ya suka ƙi shiga ramin, to za ta yi gaggawar ambatar: “hure!” Yayin da ɗaya daga cikin abokan wasanta ta riga ta ambatar hure, to ita za ta karɓi yi, ko da kuwa ba yin ta ba ne. Ke nan ta tsallake waɗanda suke layi.

A ɗaya ɓangaren kuma, mai wasa za ta iya yin tsakure, wato ta jawo‘ya’yan da ba su kai yadda za ta ɗauke yawan ‘ya’ya daidai da yin da take ba; misali ta jawo‘ya’ya biyar kaɗai yayin da take biyarwa, ko ‘ya’ya shida yayin da take bakwalwa. A irin wannan yanayi za a iya cewa: “Kin tsakuro mayyarki!” Idan a ɗayalwa take, sai kuma ta tsakuro ɗaya kaɗai, za a ce: “Ɗayarki mayya.” Idan kuwa tana biyulwa, sai ta tsakuro biyu kaɗai, to za a ce: “Biyunki mayu! …”

Bayan haka, yayin da mai wasa ta yi satar gaba, wato ta tura ɗa ko ‘ya’ya har suka wuce cikin rami zuwa gaban wata, to ta yi kuskure. Wannan ya danganta da idan wasar tana satar gaba ko ba ta satar gaba. Idan tana satar gaba, to mai wasa za ta dawo da ‘ya’yan cikin rami. Idan kuwa ba ta satar gaba, to ta faɗi.

Yayin da yarinya ta gama randunanta gaba ɗaya, to ta fita ke nan. Sai ta sa wa sauran‘yan wasa namujiya. A haka za a riƙa fita ɗaya bayan ɗaya har kowa ya fice a saurar yarinya ɗaya. Wannan yarinyar da ba ta fita ba za ta sha zolaya. Idan kuma wasar ‘yar dala ce, to za a daddale ta a matsayin sakamakon wasa.

Idan wasar ba ta masar baba ne, to da zarar mai wasa ta gama gomalwa ta fita. Amma idan tana masar baba ne, wadda ta gama gomalwa za ta jera‘ya’yan ramel a gewayen bakin rami, sannan ta riƙa jefa ƙodo sama tana tura su ɗaya bayan ɗaya. Idan ta yi nasarar tura su tsaf, to ta fita. Idan kuwa ta kasa ko ɗaya ta yi rawa a yayin torawa, to ta faɗi, kuma sai ta sake daga gomalwa.

3.14.4 Sakamakon Wasa

‘Yar ramel takan kasance mai sakamako ko marar sakamako. Tun kafin a fara wasa za a sanar da hakan ta hanyar furta ko dai ‘yar dala ce ko kuma ba ‘yar dala ba. Don haka duk yarinyar da ke tsoron wannan sakamako idan ta ji ‘yar dala ce, to ba za ta shiga ba.

Akan mayar da dukkanin ‘ya’yan da aka yi wasa da su cikin rami. Daga nan sai a mai da ƙasa a bisne su. Daga nan yarinyar da za a dala za ta ɗora tafin hannunta a kai. Wacce ta fara fita ita ce za ta fara dalarta. Za ta dunƙule hannunta sannan ta doki hannun yarinyar da ke kan wannan rami da aka bisne ‘ya’yan ramel a ciki. Kafin a fara wasa za a ƙayyade yawan dalar da kowa za ta yi. Wani lokaci masu wasa za su tausaya wa wadda ake dala, ko dai su yafe mata ko kuma su rage adadin dalar, ko kuma su sassauta zafinsa.

3.14.5 DokokinWasa

Dokokin wannan wasa ya bambanta-daga wuri zuwa wuri. Amma duk da haka an kawo wasu daga cikin dokokin wannan wasa:

i. Wadda ta kasa cafe ƙodonta ta faɗi.

ii. Wadda ta yi tsakure ta faɗi.

iii. Wadda ta yi satar gaba aka riga ta faɗin fure to ta faɗi.

iv. Wadda ta yi satar gaba a wasar da ba ta fure, to ta faɗi.

v. Wadda ta riga cewa fure ga mai satar gaba ita ce za ta karɓi yi ko da yinta bai zo ba.

vi. Wadda ta faɗi a masar baban ne sai ta sake daga gomalwa yayin da yenta ya gewayo.

vii. Wasan zai iya kasancewa ‘yar dala ko wace ba ‘yar dala ba.

viii. Yayin da ɗa ya ɓata lokacin da ake wasa, dokar tana daidai da na satar gaba.

3.14.6 Tsokaci

Wannan wasa yana koyar da natsuwa da kuma lissafi. Duk wadda ba ta nitsu ba, to za ta karya dokokin carafke, sannan ba za ta lura da satar gaba ko ɓatar ɗa ba. Sannan wasan na Koyar da ƙwarewa ga sarrafa hannu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments