Ticker

6/recent/ticker-posts

Ruwa Mai Malale

6.13 Ruwa Mai Malale

Wannan ma wasa ne da ‘yanmata ke gudanarwa wadda ba na tashe ba. An fi yin sa da dare, musamman lokacin farin wata. Hasali a dandali ake wasan, amma yakan kama a yi a cikin gida mai fili ko kuma a ƙofar gida.

6.13.1 Yadda Ake Wasar Ruwa Mai Malale

Yara sukan yi da’ira mai ɗan faɗi ta hanyar barin‘yar tazara a tsakanin junansu. Daga nan ɗaya daga ciki za ta shigo tsakiya. Za ta fara ba da waƙa yayin da saura ke amsawa. Sannan yaran za su riƙa tafi yayin da ake wannan waƙa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Ruwa mai malalae,

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: ‘Yar yarinya,

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: Ke wa kike so?

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: Ɗan farin yaron nan,

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: Wanan ɗan gayen nan,

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: Mai kyawu da riga,

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: Mai kyawu da wando,

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: Mai kyawu da hula,

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: Mai kyawun takalmi,

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: Shi ne take so,

Amshi: Ɗagogwarago.

 

Bayarwa: Ai ta gaya min,

Amshi: Ɗagogwarago.

Bayarwa: Shi za ta aura,

Amshi: Ɗagogwarago.

6.13.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi da annashuwa ga yara. Sannan waƙar wasana ɗauke da wani saƙo zuwa ga iyayensu da kuma sauran mutanen gari. Wannan saƙo ya ƙunshi bayyana cewa sun fara soyayya, ko irin muradinsu na aure da dai makamantansu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments