Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba Mu Kudinmu

5.10 Ba Mu Kuɗinmu

Wannan wasa ne na tashe wanda yara maza ke gudanarwa. Kimanin mutane biyar ne zuwa sama da haka suke gudanar da shi. Sannan akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da wannan wasa. Kasancewar sa wasan tashe, an fi yin sa da dare, bayan an sha ruwa.

 

5.10.1 Kayan Aiki

i. Filo/matashin kai

ii. Sanduna marasa nauyi sosai ko tsumagu

 

5.10.2 Yadda Ake Wasa

Yara za su goya wa ɗaya daga cikinsu filo guda ɗaya ko biyu. Wannan ya danganta da girman filon. Domin buƙata shi ne, yayin da aka doki wannan yaro, kada ya ji zafin dukan. Kowanne daga cikin sauran yara kuwa zai nemi ƙatuwar tsumagiya, ko ma sanda marar nauyi ya riƙe.

Yayin da ake wurin wasa, waɗannan yara za su hau dukan wannan da suka goya wa filo. Shi kuwa zai riƙa sanya waƙa, saura na amsawa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Wayyo Allah!

Amshi: Ba mu kuɗinmu.

 

Bayarwa: Wanne kuɗinku?

Amshi: Kuɗinmu na bashi.

 

Bayarwa: Bashin mene?

Amshi: Bashin doya?

 

Bayarwa: Na doyar yaushe?

Amshi: Na doyar bara.

 

Bayarwa: Ta nawa kuka bani?

Amshi: Ta dala muka ba ka.

 

Bayarwa: A ina kuka ba ni?

Amshi: Ɗakin Baba.

 

Bayarwa: Ina shaidarku?

Amshi: Mu je gun Inna.

 

Wannan ɗa na ƙarshe akan faɗe shi ne idan a cikin gida ake wasan. Idan kuwa a dandali ne, wurin maza, yaran kan ce:

Bayarwa: A ina kuka ba ni?

Amshi: Ɗakin Inna.

 

Bayarwa: Ina shaidarku,

Amshi: Mu je gun Baba.

 

Hikimar hakan shi ne, yayin da aka ce a je wurin inna a cikin gida, za a je wurin da mata ko matan gidan suke tsaye ko zaune ne. A dandali kuwa, idan aka ce mu je gun baba, to za a matsa ne kusa da wurin wanda ake wa tashe. Daga nan kuma sai su ci gaba da waƙar:

Bayarwa: Wayyo Allah!

Amshi: Ba mu kuɗinmu.

 

Bayarwa: Ku tsaya in ba ku,

Amshi: Sai ka ba mu.

 

Bayarwa: Ni fa ɗangata ne,

Amshi: Ina gatarka?

 

Bayarwa: Ga shi ubana?

Amshi: To ya ba ka ka ba mu.

 

Bayarwa: Baba ba ni in ba su,

Amshi: Da dai ya fi.

 

Bayarwa: Baba za su kashe ni,

Amshi: Sosai-sosai.

 

Bayarwa: Baba ba na fa jigata,

Amshi: Sosai-sosai.

 

Bayarwa: Baba har da gumi fa,

Amshi: Sosai-sosai.

 

5.10.3Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Sannan yana nuni ga munin wata ɗabi’a ko hali, wato cin bashi. Wanda wannan hali na kai mutum ga wulaƙanta kamar dai yadda mai cin bashin doyar nan ya wulaƙanta. Baya ga haka, wasan na nuna tabbatar da kasancewar iyaye gata ga ‘ya’yansu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments