Ticker

6/recent/ticker-posts

5.7.10 Waƙar Tatsuniyar Ɓaure Mai Magana - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 130)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

5.7.10 Waƙar Tatsuniyar Ɓaure Mai Magana

Yarinya: Girgije-girgije na zo gare ka,

Girgije: ‘Yar nan na ba ki me?

Yarinya: Na zo ka ba ni ruwa,

Girgije: Ruwan ki kai wa wa?

Yarinya: Ruwan na ba ciyawa,

Girgije: Ciyawar ta ba ki me?

Yarinya: Ciyawa ta ba ni ganye,

Girgije: Ganye ki kai wa wa?

Yarinya: Ganye na kai wa Nagge,

Girgije: Naggen ta ba ki me?

Yarinya: Nagge ta ba ni kashi,

Girgije: Kashin ki kai wa wa?

Yarinya: Kashi na kai wa Ɓaure,

Girgije: Ɓaure ya ba ki me?

Yarinya: Ɓaure ya ba ni ‘ya’ya,

Girgije: ‘Ya’yan ki kai wa wa?

Yarinya: ‘Ya’ya na kai wa Inna,

Girgije: Inna ta ba ki me?

Yarinya: Innar ta ba ni zanna,

Girgije: Zanna ki je ina?

Yarinya: Zanna na je ni wasa, tsara duka sun tafi.

(Yahaya, 1982: 67)

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments