Ticker

6/recent/ticker-posts

Waɗansu Muhimman Abubuwa Da Masana Halayyar Ɗan'adam Suka Bayyana Game Da Tarbiyyar Yara

1 - Zagin Yaro kullum na sa ya lalace.

2 - Tsangwama ga Yaro na jawo masa rashin walwala.

3 - Kushe Yaro kullum na sa shi ya raina kansa.

4 - Kunyata Yaro n asa shi ya dinga ɗari-ɗari da kansa.

5 - Koya wa Yaro juriya na sa shi ya zama mai haƙuri.

6 - Idan ana yaba Yaro yakan tashi da kishin zuci.

7 - Idan ana kyautata wa Yaro yakan sanya shi ya zama mai gaskiya.

8 - Tarbiyya ga Yaro takan sanya shi ya zama amintacce.

9 - Idan aka amince da Yaro yakan sanya shi ya ji daɗi.

10 - Sakin fuska ga Yaro shi ke jawo shi cikin Jama'a. 

Iyaye sai mu kiyaye.

 Allah ya shiryar mana da zuri'armu, amin.

Post a Comment

0 Comments