Ticker

6/recent/ticker-posts

Sallar Kwadi

5.40 Sallar Kwaɗi

Wannan ma wasa ne da yara maza ke gudanarwa. Yawanci yara kimanin goma zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. Yana kama da wasan ɓelunge a zubi da tsari, kasancewar wasan na da tsarin shugabanci irin na liman da ladan da kuma mamu. An fi gudanar da wannan wasa a dandali, da dare musamman lokacin farin wata.

5.40.1 Kayan Aiki

i. Riguna waɗanda aka nannaɗa su domin dukan wanda ya ɓata wasa.

ii. Bishiya ko garu ko wani abu a matsayin sha.

5.40.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan naɗa liman da kuma ladan. Saura kuma za su kasance a matsayin mamu. Liman zai tsaya a gaba, amma zai juyo ya riƙa kallon mamu. Ladan kuma zai tsaya tsakanin liman da mamu. Mamu kuwa za su jeru sahu-sahu daidai da yawansu. Daga nan liman zai riƙa abubuwan dariya iri-iri. Duk abin da ya faɗa dole ne ladan ya maimaita duk wahalar zancen ko tsawonsa. Da zarar ladan ya maimaita, sai mamu ma su maimaita.

Yayin da ake wannan wasa, duk wanda ya yi dariya daga kan liman har ladan har mamu, to za a bi shi da duka. Ba za a bar shi ba har sai ya sha. Haka ma idan wani ya yi magana ba lokacin da ya dace ya yi ba. Misali idan ladan ya yi magana kafin liman ya gama. Ko idan mamu suka yi magana kafin ladan ya ƙare magana. Haka ma idan liman ya yi magana kafin mamu su kamala magana. Duk wanda ya ɓata wasa, kuma ya je ya sha, to shi ne zai zama liman. Misalin irin karatun da ake yi a sallar kwaɗi shi ne:

Nai haka,

Nai haka,

Na buga tusa bot!

Yayin da liman ya faɗi wannan magana zai botsare tamkar dai ya yi tusar gaske. Haka ma ladan zai yi, sannan mamu. Abin zai ba wa mai kallo dariya, Amma su masu wasa, dole ne su cije dariya gudun shan kashi (duka).

5.40.3 Wasu Dokokin Wasa

i. Ba a yarda wani ya yi dariya ko tari ba.

ii. Ba a yarda wani ya yi magana ba a lokacin maganarsa ba.

iii. Dole ne ladan ya faɗi dukkanin abin da liman ya faɗa duk tsayi da wahalarsa.

5.40.4 Tsokaci

Wannan wasa na koyar da halayyar nitsuwa da kuma rashin wuce makiɗi da rawa a cikin salla. Sannan hoto ne ko madubi da ke hasko tsarin shugabanci da gudanarwar salla.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments