Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yar Ganel

5.27 ‘Yar Ganel

Wannan ma wasa ne na yara maza da ake gudanarwa a dandali. An fi gudanar da wasan da dare, musamman lokacin farin wata. Sai dai a wasu lokuta akan yi shi da hantsi ko da yamma. Kayan aikin da ake buƙata kawai su ne riguna da kuma wurin sha. Wato kowane yaro na yin amfani da rigarsa. Sannan wasan ba ya tafiya da waƙa.

5.27.1 Yadda Ake Wasa

A wannan wasa, akan samu sarki da kuma bafaɗe, sai kuma sauran ‘yan wasa. Sarki zai koma can gefe guda ya zauna. Sauran ‘yan wasa kuwa za su taru wuri guda, su ma a zaune. Bafade kuwa zai kasance yana mai zirga-zirga tsakanin sarki da sauran ‘yan wasa. Shi ke ɗauko saƙo daga sarki zuwa wurin ‘yan wasa.

Bayan kowa ya natsu, bafade zai je wurin sarki. Sarki kuwa zai raɗa masa sunan wani abu a kunne. Wannan abu zai kasance gida ko bishiya ko unguwa ko wani mutum mai muƙami da dai sauransu. Sannan zai faɗi takamaimai wane abu yake nufi. Misali idan bishiyar dabino ce, zai yi furuci kamar haka:

“Bishiyar dabinon gidansu Musa.”

Idan unguwa ce kuma, zai ce:

WASANNI A ƘASAR HAUSA

“Unguwar Nasarawa.”

Idan kasuwa ce kuma, zai iya cewa:

“Kasuwar Kurmi.”[ Kurmi kasuwa ce da ke garin Kano. An kawo ta ne a matsayin misali kasancewar tana ɗaya daga cikin sanannun kasuwanni.]

Daga nan bafade zai zo wurin ‘yan wasa. Idan misali bishiyar mangoro sarki ya faɗa masa; zai ce da ‘yan wasa:

“Bishiyar mangoro, bishiyar mangoro.”

‘Yan wasa kuwa za su fara ba da amsa ɗaya bayan ɗaya, bisa ƙa’idar layin da suke zaune. Wato idan guda ya yi magana, sai na gefensa ma ya yi. Misali:

Na farko: “Mangoron gidansu Audu”

Na biyu: “Mangoron gidansu Babayo”

Na uku: “Mangoron kantin Bala”

Haka dai abin zai ci gaba har sai kowa ya faɗi ra’ayinsa. Yayin da kowa ya ƙare, sai bafade ya ware wanda ko waɗanda suka yi nasara. Za a tafi da su fadar sarki. Idan kuwa babu wanda ya yi nasara, bafade zai bayyana musu bishiyar mangoron da ake nufi. Misali:

“Mongoron gidansu Abbati na muku bol,

Ya muku bolin-bolin bol!”[ Yayin da zai furta ‘bol’, zai juya musu baya ya botsare musu ɗuwawu tamkar dai wanda ya musu tusa.]

Haka wasa zai ci gaba da kasancewa har sai kowa ya samu nasarar gane tambaya, ya rage saura mutum guda. Za a sake yi masa tambaya guda ɗaya. Idan ya gane to ya ci sa’a. Idan kuwa bai gane ba, yara za su bi shi da duka ta amfani da riguna da suka nannaɗa. Yaron kuwa zai yi ta gudu yana faman sha. Da zarar ya sha, za a ƙyale shi. Sannan shi ne zai kasance sarki yayin da za a koma wasan.

5.27.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan ta dalilin wasan, yara na sanin gidajen da suke unguwanni, da kuma nau’ukan bishiyoyi da ke zagaye da su. Bayan haka, yara na sanin sunayen muhimman wurare da ke garinsu. Sannan wasan na koyar da jarumta da zurfafa tunani ga yara.

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments