5.26 Taka Ɓurme
Wannan ma wasa ne na yara maza. An fi yin sa lokacin damina, yayin da ƙasa ke da damshi. Wani lokaci kuwa akan gudanar da ita a kan yashi. Wato yashin da aka kawo aka zube domin a yi ginin bulo na siminti. An fi gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma. Ba a faye yin sa da dare ba.
5.26.2 Kayan Aiki
i. Tsinkaye
ii. Ledodi
iii. Abin tonon rami
5.26.2 Yadda Ake Wasa
Yara za su tona rami mai ɗan madaidaicin zurfi. Tsawonsa yana kasancewa wanda ba zai wuce rabin ƙwabri ba. Sai kuma su gindaya tsinkaye masu ɗan ƙarfi a saman ramin. Daga nan kuma za su shimfiɗa ledodi saman tsinkayen, su rufe ko ina. Za kuma su riƙa zuba ƙasa a hankali saman waɗannan ledodi. A haka har sai sun zuba ƙasa a ko’ina, yadda ba a ganin ledodin. Wanda bai san akwai rami a wurin ba, ba zai taɓa ganewa ba.
Yayin da taka ɓurme ya kammala, sai yara su fara neman mai faɗawa. Yayin da wani daga cikin abokansu ya zo wucewa, za a yaudare shi da magana har sai ya biyo ta wurin da aka yi taka ɓurme. Da zarar ya taka kuwa, sai tsinkayen da aka ɗora bakin ramin suka rairaye, ya faɗa ciki. Yara za su yi dariya da shewa. Daga nan kuma a sake gyara taka ɓurme.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.