Ticker

6/recent/ticker-posts

Goga

 5.2 Goga

Wannan ma wasan maza ne da aka fi gudanarwa da kaka’a, wato bayan an girbe amfanin gona. Yara da matasa duka suna irin wannan wasa. Akan yi wasan tsakanin mutane biyu ko sama da haka (har zuwa kowane adadi).

5.2.1 Lokaci Da Wurin Wasa

i. Ana gudanar da wannan wasa da kowane irin lokaci, wato hantsi ko da yamma ko da dare.

ii. Babu wani ƙayyadadden wuri da ake gudanar da wannan wasa. Akan yi wasan a duk wurin da yara (masu wasan) suka haɗu; kamar dandali, ko ƙofar gida ko ma cikin gida da makamantansu.

5.2.2 Kayan Aiki

i. Gaɓar karan dawa ko na masara

ii. Reza ko wuƙa ko wani abu mai kaifi

 

5.2.3 Yadda Ake Gudanar DaWasa

Yara na zaɓo gaɓar karan dawa ko masara mai ƙarfi ƙwarai. Sai kuma su ɓare gefe ɗaya na karan; wato su bar gefe ɗaya da ɓawonsa. Daga nan za su yi amfani da reza ko wuƙa ko wani abu mai kaifi su fafake daidai ƙasa da kan gaɓar karan. Wato su samar da ɗan rami a wurin, daidai yadda idan aka haɗa gaɓar kara guda biyu, kan gaɓoɓin karan guda biyu za su shiga ramukan da aka fafake a jikin juna; wato tamkar dai an haɗa ƙugiya da ƙugiya.

 

Yayin gudanar da wasan goga, yara biyu za su maƙala gaɓar kararen da ke hannunsu a jikin juna. Wato su lanƙaya a jikin ramukan da aka fafake a jikin gaɓar karan juna. Daga nan za a ƙirga ɗaya zuwa uku, sai a ja da ƙarfi. Duk yaron da kan gaɓar karansa ya ɓalle yayin da ake ja, to ya faɗi a wasa. Yaron da ya yi nasara to gaɓar karansa ya zama goga. Wannan yaro zai riƙa taƙama yana cewa: “Wa zai kara da goga?’”

 

Wasu lokuta akan yaɗa ƙungiya-ƙungiya. Saboda haka, ƙungiya ɗaya za su tari wata ƙungiya a karawar goga. Waɗanda gogayensu suka fi ƙarfi za su kakkarya gogayen abokan karawar su. Wani lokaci kuma, yaran wata unguwa ne ke tarar wata unguwa a wannan wasa na goga.

 

5.2.4 Tsokaci

Wannan wasa yana koyar da jarumta. Sannan yana siffanta yaƙi, kamar yadda ƙungiya ke tinkarar ƙungiya, ko kuma ‘yanunguwa ke tunkarar ‘yan wata unguwa domin a gwabza gasar goga.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments