Ticker

6/recent/ticker-posts

Gori/Koɗi 1

 5.3 Gori/Koɗi 1 (Na Gargajiya)

Sunan wannan wasa ya samo asali daga wata dabba mai suna dodon gori ko dodon koɗi. Wannan dabba sananniya ce a ƙasar Hausa. Tana da wani ƙoƙo wanda cikinsa take rayuwa. A nan ƙoƙo ba shi da kauri sosai. Sannan kewayayye ne, mai tsini a ƙarshensa. Yara biyu ne ko sama da haka suke wannan wasa.

5.3.1 Lokaci Da WurinWasa

i. An fi aiwatar da wannan wasa da hantsi ko kuma yamma. Wato ba a faye yin sa da dare ba.

ii. Da yake bai zama dole yara da yawa su taru kafin gudanar da wannan wasa ba, babu wani ƙayyadadden wurin da ake gudanar da shi. A maimakon haka, yara na gudanar da shi a wurare kamar dandali ko ƙofar gida ko ma cikin gida.

5.3.2 Kayan Aiki

i. Ƙoƙon dodon koɗi wadda aka yanke saman (wurin da ke da faɗi) aka daidaita shi.

 

5.3.3 Yadda Ake Wasan Koɗi

Akan sami ƙoƙon dodon koɗi a yanke saman domin a daidaita shi. Daga nan masu wasa za su zauna a da’ira, suna fuskantar juna. Mai riƙe da koɗi zai gara a ƙasa. Yayin da koɗi ke ta faman garuwa a ƙasa, yaron zai yi amfani da ƙwarewa wajen kifar da shi cikin hikima. Wannan kuma ya danganta da salon kifarwa da yaran suka sanya a matsayin dokar gasa. Wato ko dai ta hanyar amfani da hannuwa biyu. Ko kuma hannu ɗaya kaɗai, ko ma yatsa biyu ko ɗaya. Yayin da yaro ya kife koɗi, to ya ci ke nan. Sai kuma yaro na gaba ya karɓa. Wasu lokuta akan sanya gasar dokar ta kasance sai yaro ya kife koɗi sau biyar ko goma ko ma sama da haka kafin ya ci. Yayin da haka ta kasance, ko da ya kife sau tara, sai kuma ya faɗi a na goma, to bai ci ba.

 

Yayin gudanar da wannan wasa, duk wanda ya ci, to ya fita ke nan. Sai ya zuba wa saura idanu. A haka za a yi ta fita ɗaya bayan ɗaya, har a kan ga na ƙarshe. A nan za a sake ba shi damar sake gwadawa sau ɗaya. Idan ya ci sa’a ya kife koɗi, to ya tsira. Idan kuwa bai kife ba, to sakamakon wasa ya hau kansa. Bayan an ƙaddamar da sakamakon wasa kuwa a kan wanda ya faɗi, shi ne ke da hurumin fitar da sabbin dokokin wasa. Misali, idan da ana kife koɗi ne da hannu ɗaya. Zai iya cewa, yanzu sai an kife da yatsa ɗaya kafin a yi nasara. Sannan zai iya canza sakamakon wasa (wato hukuncin da za a zartar wa wanda ya faɗi).

 

5.3.4 Sakamakon Wasa

Wasan koɗi na da sakamako da ke biyo bayan kowane zagayen wasa. Wannan kuwa wani hukunci ne da ake zartarwa wanda ya faɗi a zagayen wasan da ya gabata. Wanda ya faɗin na sanya tafin hannunsa a ƙasa, wato bayan hannunsa yana sama. Daga nan sauran yara za su riƙa amfani da koɗi suna rankwaɗa masa a kan bayan hannun. Ana kiran hakan da ci ko sha. Yawan shan da kowanne yaro zai yi wa wanda ya faɗi ya danganta ga dokar da aka sanya na sakamakon wannan zagayen wasa. Akan samu lokutan da har bayan hannun wanda ake sha ya riƙa jini. Yayin da jini ya fito a bayan hannun yaron da ake sha, akan ce an fitar masa jatau. A wasu lokuta, dokar takan nuna cewa, duk wanda ya je shan wanda ya faɗi gasa, sai aka yi rashin sa’a bai samu bayan hannun ba (wato koɗi ta rankwaɗu a ƙasa), to kuwa wanda ya faɗi gasar ya tsira. A maimakon a ci gaba da masa hukunci, za a ƙarasa hukuncin a kan wannan yaro da ya sha ƙasa a maimakon shan bayan hannu.

Bayan haka, wanda ya nuna zai fita ba tare da an kamala wasa ba, to za a masa cin fita. Tun farko za a ƙayyade cin fita guda nawa ne.

5.3.5 Tsokaci

Haƙiƙa wasan koɗi na ɗaya daga cikin wasannin yara mafiya tsaurin dokoki da kuma sakamakon wasa. Wannan wasa na sanya wa yara jarumta, kasancewar wanda ya faɗi dole ya juro shan da za a yi masa a matsayin sakamakon wasa. Sannan wasan na koyar da bin doka, kasancewar dole ne yaro ya riƙe dokokin wasa sau da ƙafa, karya ɗaya daga cikin dokokin na kaiwa ga hukunci. Bayan haka, wasan na koyar da ƙwarewa da naƙaltar fasahar sarra fahannu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments