Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
5.10 Girmama Ma’auraci
Al’adar Bahaushe ce girmama mutum
mai aure mace ko namiji. Sau da yawa idan ana yi wa mai sabon aure huɗuba akan lurar da shi yanzu fa ya
shigo cikin dattawa. Wannan tunanin ne da ke ga Bahushe na cewa aure shi ne
matakin zamowar mutum dattijo kamar yadda hakan ke bayyana a cikin wasu waƙoƙi na mabarata
ta hanyar kiran kowace mata da ke gidan aure Inna. Duk wata waƙa ko bara da almajiri zai yi, zai ambaci matar gida da
sunan Inna ko da kuwa mai baran ya gimi matar da ke gidan da ake baran. Misali:
A tumbulo Inna
a tumbulo,
A tumbulo a kawo
ma gajere,
Gajere ba abin reni ne ba.
Da kuma:
“Ya ta’ala lillahi
almajirin bara,
Inna ina bara kina ƙyale ni, ko ɗanɗanki nit taɓa”.
Duk waɗannan ɗiyan waƙa da aka ambata sama suna nuni ga bayar da girma ga matar
da ke da aure wadda ita ce almajri ke zance da ita sadda yake bara ko da kuwa ƙaramar yarinya ce wadda da a kan hanya zai haɗu da ita da ba zai ba ta wannan
girma ba. A nan ma wata falsafar zamantakewa ta Bahaushe ta shigo a cikin waƙoƙin na bara.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.