Ticker

6/recent/ticker-posts

5.11 Lalama Ga Mai Nema

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.11 Lalama Ga Mai Nema

Falsafar biɗa/nema ce a saka hattara da lallaɓawa ga neman abu domin a sami biyan bukata cikin sauƙi. Tunanin sanin haka ya sa almajirai ke nesanta kansa daga kowane irin amfani da ƙarfi. Shi mai neman a ba shi ne, don haka ya yi wa mata masu riƙe da ragwama a cikin gida da lalama tare da nuna yanke hulɗa da duk wani mai iya nuna ƙarfi ga neman biyan bukatarsa. Ga abinda wata waƙar bara ke cewa:

 Ya Allahu Ya Tabaraka ya Rabbana.

 Kura ta ga ɗan bara ɗan almajiri.

 Bari in bi ka ɗan bara in shawo gari.

 Tahiyata da taki ba ta zama ɗai da ɗai.

 Ni roƙo ni kai ga mata ‘yan arziki.

 Ke ƙwace ki kai ga mata ba su ba ki ba.

 (Ya Tabaraka ya Rabbana)

A waɗannan ɗiyan waƙa mai bara ya nisantar da kansa daga haɗa tafiya da kura. Dalilin haka kuwa shi a cikin lalama yake neman bukatarsa kuma ta biya. Ita kuwa kura ba tarar lalama take ba da ƙarfi take ƙwace, don haka hanyar mota daban ta jirgi daban. A nan mai bara na nuna akwai alaƙa mai kyau tare da fahimtar juna tsakanin almajirai da mata. Wannan wani tunanin rayuwa ne da Bahushe ya amince da shi na cewa mai neman abu da lalama yake nemansa sai ya samu biyan bukata. Wanna Tunani ya yi daidai da maganar hikimar Baushe da ke cewa “Duk abinda girma da arziki bai bayar ba, to tsiya ba ta byar da shi.”


Post a Comment

0 Comments