Ticker

6/recent/ticker-posts

5.9 Dangantakar Almajirai Da Mata.

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.9 Dangantakar Almajirai Da Mata.

Idan an ce dangantaka ana nufin hulɗa ko alaƙa a tsakanin wani mutum da wani. Bara Almajirai mafi yawa bai wuce na sarrafaffen abinci ba. Shi kuwa sarrafaffen abinci a Hausance hannun mata yake. Wannan shi ya kawo danganta mai ƙarfi tsakanin Amajiri da mata. Irin yadda Almajirai ke yawan ambaton mata a cikin waƙoƙinsu tare da nuna alaƙa da su na nuna irin tunanin Bahaushe game da kasancewar mata su ne masu riƙe da gida. Duk da ɗan gida sai matar gida ta so yake wadata da abinci, idan ba ta so ba tana iya yi masa munaƙisa. Wannan shi ya sa koyaushe ake ganin waƙoƙin bara na nuna yin fadanci ga mata. Misali a cikin waƙar “Lansika” inda ake cewa:

Jagora: Mata dangin Fatsima,.

Amshi: Kulle.

Jagora: Ku taru ku ba mu na Annabi.

Amshi: Kulle.

 (Mata Dangin Fatsima)

A lura a ɗiyan da suka gabata yadda mai bara ke fadanci ga mata duk da yake yana sane abin nan da yake bara yake son a ba shi ga haƙiƙa ba mallakar matar gida ba ne mallakar mai gida ne, amma amincewar da tsarin rayuwar Bahaushe ta yi na kasancewar matar gida mai mallakar sarrafaffen abinci, shi ya sa fadanci Almajiri yake ga matar gida ba mai gida ba, domin bukatarsa ta sarrafaffen abinci ce. Wannan nuni ne ga tsarin da Bahushe ya amince da shi na saka tafiyar da lamurran cikin gida ga hannun matan gida. Sanin haka ya sa Almajiri kyautata dangantakarsa da mata fiye da maza a cikin waƙoƙinsa na bara. Wannan wata falsafa ce mai nuna tsarin tafiyar da gida a cikin al’ummar Hausawa musamman ta fuskar abincin da aka sarrafa.


Post a Comment

0 Comments