Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
4.9.2.1 Baka
Jagora : Assalamu alaikum masu gida muna muku
sallama,
Amshi : Baka.
Jagora : Muna muku sallama don ɗai ku ba mu na Annabi,
Amshi : Baka.
Jagora : Sai zuciya ta daure in zuciya ta
dangana,
Amshi : Baka.
(Baka)
Almajirai kan tafi bara kamar su uku ko fiye da haka, ɗaya ne daga cikinsu kan jagoranci ƙungiyar wajen yin wannan waƙar sauran kuma suna amsawa, suna rera waƙar a gida-gida ko kuma a kasuwa ko wani wurin taruwar jama’a. Ana ba su sadakoki daban-daban kama daga abinci zuwa sutura da sauransu a lokacin da suke rera wannan waƙar.
A wata waƙar kuma wadda mabarata manyan mutane mata ke yi:
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.