Ticker

6/recent/ticker-posts

4.9.2.2 Bani Malam

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.9.2.2 Bani Malam

 Jagora: Ba ni Malam,

 Amshi: Ba ni Malam.

 Jagora: Fi sabilil lahi,

 Amshi: Ba ni Malam.

 Jagora: Don girman Allah,

 Amshi: Ba ni Malam.

 Jagora: Saboda Rasulullahi,

 Amshi: Ba ni Malam.

 (Ba ni malam)

Ita kuma wannan waƙar manyan mata ne makafi ke yin ta, sun fi tafiya baran su uku inda suke yin wannan waƙar, ɗaya tana jagora a rera waƙar sauran biyun suna amsawa. Haka suke yi suna zagayawa a tituna da kasuwanni har ma da gidaje don su sami sadaka daga masu sauraren su.


Post a Comment

0 Comments